19 ga Oktoba, 2024
1039 GMT — Jimillar mutane da yaƙin Isra'ila ya kashe a Gaza ya kai 42,500
Aƙalla Falasɗinu 19 aka halaka a harin Isra'ila a Gaza, wanda ya kai jimillar mutanen da aka kashe tun Oktoban bara zuwa mutum 42,519, cewar ma'aikatar lafiya ta yankin da ke ƙarƙashin mamaya.
Ma'aikatar ta ce wasu ƙarin mutane 99,637 sun samu raunuka sakamakon hare-haren da ke ci gaba.
“Dakarun Isra'ila sun kashe 19 sun kuma raunana mutum 91 cikin wani kisan kiyashi da suka yi wa wasu iyalai cikin awanni 24 da suka gabata,” cewar ma'aikatar.
“Wasu tarin mutane sun maƙale ƙarƙashin baraguzan gine-gine da kuma tituna, yayin da ma'aikatan ceto suka kas cim musu”.
1029 GMT — Masu ceto a Isra'ila sun ce mutum guda ya mutu sakamakon fallen bam daga Lebanon
Jami'an ceto a Isra'ila sun ce mutum guda ya mutu bayan fallen daga makamin roka da aka harbo daga Lebanon ya same shi, a birnin Acre bayan ruwan rokoki da aka harbo cikin Isra'ila daga arewacin Lebanon.
"Jami'an lafiya sune ce wani namiji mai kimanin shekara 50 ya mutu, wanda fallen bam ya same shi yana zaune cikin mot," cibiyar ceto ta Magen David Adom ta faɗa a wata sanarwa.
1011 GMT — Iran na goyon bayan zaman lafiya amma ta shirya ko me zai faru: Ministan Harkokin Waje Araghchi
Iran na goyon bayan zaman lafiya amma ta shirya ko me zai faru, in ji Ministan Harkokin Waje Abbas Araghchi.
"Yaɗuwar yaƙin a yankin wata babbar barazana; muna goyon bayan zaman lafiya amma ta shirya ko me zai faru," ministan ya faɗa wa manema labarai tare da takwaransa na Turkiyya, Hakan Fidan a Istanbul.
Duk da kokawar da ƙasashen duniya suke yi da ƙoƙarin kawo ƙarshen rikice-rikice, Isra'ila na ci gaba da kai hari ta ƙasa a Lebanon da Gaza.
0721 GMT: An kai harin jirgi mara matuƙi kan gidan Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu
Hukumomi a isra'ila sun ce wani jirgi mara matuƙi ya kai hari wajen gidan Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a garin Caesarea da ke arewacin Isra'ila, kamar yadda kakakinsa ya ambata, kuma ya ƙara da cewa firaministan ba ya wajen kuma babu wanda harin ya shafa.
Tun da fari, Sojojin Isra'ila sun ce an turo wani jirgi mara matuƙi daga Lebanon, kuma ya faɗa kan wani gini. Sai dai ba a bayyana ko wane gini ba ne.
0720 GMT — Harin Isra'ila ya kashe mutum biyu a arewacin babban birnin Lebanon
Aƙalla mutum biyu sun mutu a wani harin da Isra'ila ta kai kan wata mota a Jounieha, arewa da Beirut, cewar ma'aikatar lafiya ta Lebanon. Wannan ne harin dakarun Isra'ila na farko a yankin.
0713 GMT — Firaministan Malaysia ya yi tir da kisan shugaban Hamas Yahya Sinwar
Firaministan Malaysian Anwar Ibrahim ya yi kakkausar suka kan kisan shugaban Hamas, Yahya Sinwar.
A wata sanarwa da ya wallafa, firaminista Anwar na Malaysia ya yi jimamin rashin "jarumi kuma garkuwar al'ummar Falasɗinawa."
"Malaysia tana kausasa yin tir da kisan, kuma yanzu ya bayyana cewa gwamnatin Isra'ila tana zagon ƙasa kan buƙatar sakin fursunoni. Malaysia tana jaddada cewa ƙasashen duniya su yi alla wadai da zaluncin Isra'ila, kuma dole ta dakatar da kisan kiyashin da take yi wa Falasɗnawa," ya faɗa a harshen ƙasar.