Ma'aikatar Shari'a ta Isra'ila ta fitar da jerin sunayen Falasdinawa fursunonin yaƙi da ake tsare da su a gidajen kurkuku, wadanda za a yi musayar su da 'yan Isra'ila da Hamas ta kama a Zirin Gaza.
Yarjejeniyar da aka ƙulla ta tanadi za a yi musayar Falasdinawa 150 da suka haɗa da mata da yara ƙanana da fursunonin yaki na Isra'ila 50.
Ga dai abun da muka sani game da fursunonin yaki Falasdinawa:
Su waye fursunonin yaƙi na Falasɗinu da ke jerin sunayen?
Jerin sunayen da Ma'aikatar Shari'a ta Isra'ila ta fitar ya ƙunshi mutume 300, 123 daga ciki yara ne ƙanana. Mun yi duba zuwa ga bayanan ko su waye wadannan fursunoni na yaƙi.
Sunayen sun ƙunshi na mata 33 da ke ɗaure a kurkukun Isra'ila. An kama fursunonin a tsakanin 2021 da 2023.
Mafi ƙarancin shekaru a cikinsu shi ne ɗan shekara 14 Abdur Rahman Amer Fakhri, wanda aka kama a watan Satumban 2023 bisa zargin sa da tayar da zaune tsaye.
Mafi tsufa daga cikin su kuma ita ce Hanan Saleh Abdullah Barghouti mai shekara 59, da aka kama a watan Satumba saboda dalilan tsaro da ba a bayyana wadanne ba ne.
Wacce tuhuma aka yi musu?
Kotunan Isra'ila sun tuhumi mafi yawan fursunonin da laifuka daban-daban.
Misali, Ahmed Ali Muhammed, da aka kama a watan Yinin 2022, ya shiga kurkuku saboda jifa da duwatsu.
Abdur rahman Suleiman Ahmed dan shekara 16, da aka kama a ranar 5 ga Oktoba ya shiga kurkuku bisa zargin jifa da duwatsu.
Isra'ila ta kuma tuhumi mata da yara kanana da ke cikin jerin sunayen da laifin jifa da duwatsu, yunkurin aikata kisa, shiga iyakar Isra'ila ba bisa ka'ida ba da zama mamban kungiyoyin da ba a san su ba.
Falasdinawa nawa ne a gidajen kurkukun Isra'ila?
Kafin 7 ga Oktoba, akwai Falasdinawa 5,200 da ke gidajen kurkukun Isra'ila.
Sai dai kuma, jami'an Falasdinawa sun ce adadin ya kai 10,000 bayan da Isra'ila ta fara kai hare-hare Gaza inda ta dinga kama Falasdinawa a gaza da yammacin Gabar Kogin Jordan.
A wanne hali Falasdinawan da ke gidajen kurkuku Isra'ila ke ciki?
Kungiyar kare hakkokin dan adam ta Isra'ila B'Tselem ta ce sama da Falasdinawa 1,300 na tsare ba tare da gabatar da su a gaban kotu ba, daga ciki har da ƙananan yara 146.
Tun bayan da Isra'ila ta fara kai hari Gaza, wannan adadi ya ninninka sosai.
Jaridar isra'ila ta Haaretz a watan Oktoba ta rawaito yadda aka muzanta wasu Falasdinawa uku da ake tsare da su wadanda sojojin Isra'ila da Yahudawa 'Yan Kama Wuri Zauna suka kamo a Yammacin Gabar Kogin Jordan.
Rahoton ya ce 'yan isra'ila sun yi wa Falasdinawan tsirara daga su sai dan kamfai, suka zane su, yankar su da wukake da karafa, suka kashe taba sigari a jikin su, har ma suka yi musu fitsari.
Baya ga irin wannan cusgunawa da muzantawa, wasu falasdinawa da aka tsare su sun mutu a gidan kurkukun Isra'ila tun daga 7 ga Oktoba zuwa yau.
Hukumar Kula da Fursunonin Yaki ta Falasdinawa ta ce "Mamayar da Isra'ila ke yi na daukar wani sabon salo na yin kisan gilla ga Falasdinawa."