1700 GMT — A shirye Tel Aviv take don tsagaita wuta na kwana daya don a saki Isra'ilawa 10
Wani jami'in Isra'ila ya ce gwamnatinsu a shirye take ta ƙara tsagaita wuta na kwana guda a Gaza domin samun sakin 'yan Isra'ila 10 da ake tsare da su a yankin da aka killace.
Tashar talabijin ta 13 ta Isra'ila ta rawaito wani jami'in Isra'ila ba tare da bayyana sunansa ba, ya ce an ci gaba da gwabza fada a Gaza, kuma za a ci gaba da kai hare-hare har sai an lalata kungiyar Hamas.
Jami'in na Isra'ila ya ce "Idan har (Hamas) ta sako matanmu da aka yi garkuwa da su, za a tsagaita wuta na kwana daya (a yaƙin), kwatancen mai sauki ne."
Ya kara da cewa har yanzu Qatar na kokarin sasanta tsakanin bangaren Isra'ila da kungiyar Falasdinawa ta Hamas.
0145 GMT — Hezbollah a shirye take, yayin da yakin Isra'ila ya cigaba a Gaza – wani jami’i
Kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta ce ta yi tana sa ido sosai kuma a shirye take a yayin da yaki ya sake barkewar tsakanin kawarta kungiyar Falasdinawa Hamas da Isra'il, wanda ke kara haifar da fargabar cewa ana iya sake tayar da fadan da ake yi a kan iyakar Lebanon da Isra'ila ma.
Hassan Fadlallah, wani babban dan siyasa na kungiyar Hizbullah a wani jawabinsa da aka watsa a yau Juma'a ya ce "A kasar Labanon, mun damu da fuskantar wannan kalubale, da taka tsan-tsan, da kuma shirye-shiryen tunkarar duk wani abu da zai iya tasowa a kasarmu."
Rundunar sojin Isra’ila ta ce ta tare wani “hari ta sama” da ya tsallaka daga Lebanon zuwa cikin Isra’ila, bayan da aka yi gargadin yiwuwar samun makaman roka a wasu garuruwa da ke arewacin Isra’ila tare da tura mazauna yankin da su gudu don neman mafaka.
Kungiyar Hizbullah da ke samun goyon bayan Iran da Isra'ila sun yi musayar wuta na tsawon makonni a kan iyakar bayan da rikicin Hamas da Isra'ila ya barke a ranar 7 ga watan Oktoba - rikicin ya tsaya cik mako guda da ya gabata lokacin da Hamas da Isra'ila suka amince da tsagaita wuta, yarjejeniyar da ta kare a ranar Juma'a.
Fadlallah ya ce "Ba wanda ke tunanin cewa Lebanon ta kubuta daga wannan hari na Yahudawa masu tsananin akidar son kafa kasar Isra’ila, ko kuma abin da ke faruwa a Gaza ba zai iya shafar halin da ake ciki a Labanon ba."
0145 GMT — Iran ta yi gargadin 'fuskantar mummunan sakamako' yayin da aka koma fagen daga a yakin Gaza
Iran ta yi gargadin "sakamako mai tsanani" yayin da rikicin da ya yaƙin da ake yi tsakanin Isra'ila da Hamas ya sake ɓarkewa a yau Juma'a bayan wa'adin kwanaki bakwai ya kare.
"Ci gaba da yaƙin Washington da Tel Aviv yana nufin wani sabon kisan kare dangi a Gaza da Yammacin Kogin Jordan," in ji Ministan Harkokin Wajen Iran Hossein Amir-Abdollahian a wani sako da ya wallafa a shafin X.
Ya kara da cewa "Da alama ba sa tunanin illar da ke tattare da komawa yaƙi." Isra'ila ta zargi Hamas da karya yarjejeniyar ta hanyar yunƙurin kai harin roka jim kadan kafin a kawo ƙarshen yarjejeniyar tsagaita wutan a ranar Juma'a da karfe 0500 agogon GMT.
Wata majiya da ke kusa da Hamas ta shaida wa AFP cewa reshen kungiyar da ke dauke da makamai na rundunar Qassam ya samu "umarni na komawa yaki" da kuma "kare Gaza".
1237 GMT — UNICEF ta yi kashedin 'kashe-kashe' a Gaza
Ana bukatar "tsagaita wuta mai dorewa" tsakanin Isra'ila da Falasdinu, kamar yadda mai magana da yawun UNICEF ya yi kira, sa'o'i bayan dakatar da ayyukan jinƙai da kawo ƙarshen yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, lamarin da ya jawo wasu munanan hare-haren Isra'ila jim kaɗan bayan ƙrewar wa'adin.
"Dole ne a aiwatar da tsagaita bude wuta mai ɗorewa. Babu wata mafita da ta wuce hakan, musamman ga mutanen da ... kamar yadda wani Bafalasdine ya ce ... suke cikin mummunan yanayi," in ji James Elder. Karin hare-hare a Gaza ba zai haifar da komai ba illa kisan gilla.
Yana mai cewa an fara kai sabbin hare-haren bama-bamai Gaza "masu tsanani sosai" dakikoki bayan kawo karshen yarjejeniyar tsagaita wuta, ya jaddada cewa: "Rashin yin wani abu don (samun tsagaita wuta) daga tushe tamkar amincewa a kashe yara ne."
1156 GMT — An kashe sama da Falasdinawa 60 a hare-haren Isra'ila a Gaza
Ma'aikatar Lafiya a Gaza ta ce sama da mutane 60 ne suka mutu sakamakon ci gaba da gwabzawa tsakanin Isra'ila da Hamas bayan ƙarewar wa'adin tsagaita wuta.
A cikin wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar ta ce ta kuma tattara "sauran mutane da dama a suka jikkata a harin da aka kai ta sama kan fararen hula".
1003 GMT — Isra'ila ta wallafa taswirar da ta raba Gaza zuwa 'tudun-mun-tsira’
Rundunar sojin Isra'ila ta fitar da wata taswira da ta karkasa yankin Gaza zuwa daruruwan rukunai sannan ta umarci mazauna yankin su yi nazarinsa domin ganin inda za su iya guduwa domin tsira.
An gididdiba Gaza zuwa layi da tituna a wasu bangarori na taswirar. An wallafa taswirar awanni bayan Isra'ila ta ci gaba da kai hare-hare bayan wa'adin yarjejeniyar tsagaita wuta ta mako guda da Qatar, Masar da Amurka suka shiga tsakani ya zo karshe.
Kafin tsagaita wutar, yakin ya fi zafi ne a arewacin Gaza, inda Isra'ila ta aike da dakaru ta kasa. sai dai yanzu, da alama yakin ya mayar da hankali kudancin Gaza, inda Falasdinawa kusan miliyan 2 suke zaune, ciki har da wadanda suke tsere daga arewaci.
0659 GMT — Ana 'ci gaba' da tattaunawa duk da hare-haren da Isra'ila ke kaiwa a Gaza
Qatar da Masar suna ci gaba da shiga tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas ta Falasdinawa duk da sabbin hare-haren da dakarun Isra'ila suka kaddamar da safiyar Juma'a a Gaza, kamar yadda wata majiya ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
"Qatar da Masar na ci gaba da shiga tsakani domin yin sulhu duk da cewa Isra'ila ta sake kaddamar da hare-hare a Gaza," a cewar majiyar wadda ba ta so a ambaci sunata saboda sarkakiyar lamarin, bayan an jwashe dare ana tattaunawa wadda ta gaza cim ma matsaya don tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta zuwa kwana na takwas.
A gefe guda, wata sanarwa da Ma'aikatar Wajen Qatar ta fitar ta bayyana matukar takaici kan hare-haren da Isra'ila take ci gaba da kaiwa a Gaza, tana mai cewa "sabbin hare-haren da Isra'ila ke kaiwa a Gaza suna dagula yunkurin shiga tsakani."
0607 GMT — Isra'ila ta kashe mutane da dama bayan wa'adin yarjejeniyarta da Hamas ya kare
Falasdinawa akalla shida ne suka mutu yayin harin da Isra'ila ta kai ta sama a birnin Rafah da ke kudancin Gaza, kamar yadda mai magana da yawun ma'aikatar lafiya ta Falasdinu Ashraf al Qudra ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
A gefe guda, an kashe kananan yara biyu a hari ta sama da Isra'ila ta kai a Birnin Gaza, a cewar Fadel Naim, wani likita a asbitin Al Ahli, a yayin da aka ci gaba da gumurzu tsakanin Hamas da Isra'ila bayan karewar wa'adin tsagaita wuta.
Dakarun Isra'ila sun kai jerin hare-hare a gidajen kwanan jama'a a Gaza, abin da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.
Wasu majiyoyi sun ce an garzaya da gawawwaki hudu da kuma wasu mutane asibitin Abu Youssef Al Najjar da ke birnin Rafah bayan dakarun Isra'ila sun kai musu hari.
Kazalika Isra'ila ta kai hari a wani gida a sansanin 'yan gudun hijira na Al Maghazi da ke tsakiyar inda ta kashe wani Bafalasdine tare da jikkata mutum hudu. Jami'an kiwon lafiya sun tabbatar wa kamfanin dillancin labara na Anadolu wadannan hare-hare.
0500 GMT — Isra'ila da Hamas sun ci gaba da gumurzu a Gaza
Rundunar Sojojin Isra'ila ta tabbatar da cewa ta ci gaba da kai hare-hare a arewacin Gaza da jiragen yaki da tankoki da kuma jiragen ruwan soji.
Ta bayyana haka ne ranar Juma'a bayan wa'adin yarjejeniyar tsagaita wuta tsakaninta da Hamas ya kare.
Bayanai sun ce yaki ya kaure tsakanin sojojin Isra'la da Falasdinawa masu fafutuka a arewaci da tsakiyar Gaza bayan wa'adin yarjejeniyar tsagaita wuta ya kare
0250 GMT — Isra'ila da Hamas sun amince da tsawaita tsagaita wuta zuwa rana ta takwas - WSJ
Isra’ila da kungiyar gwagwarmayar Falasdinu ta Hamas sun amince da tsawaita tsagaita wuta zuwa kwana na takwas, a wata yarjejeniya da za ta ƙunshi sakin wasu ƙarin fursunonin Falasdinu da suke tsare a gidan yarin Isra’ilan, da kuma Isra'ilawan da Hamas ke garkuwa da su, kamar yadda gidan jaridar Wall Street Journal ya ambato jami'an Masar suna faɗa.
0250 GMT — Kungiyar agaji ta Red Crescent ta Falasdinu ta ce motocin agaji 65 ne suka shiga birnin Gaza na arewaci
Kungiyar agaji ta Red Crescent ta Falasdinu ta bayyana cewa, jimillar manyan motocin agaji 65 ne suka shiga birnin Gaza da kuma arewacin Gaza.
Wannan ya kawo adadin manyan motocin da aka aika zuwa 310 tun bayan da aka dakatar da ayyukan jinƙai a ranar 24 ga Nuwamba.
Sanarwar ba ta yi nuni da ko an aike da motocin man fetur zuwa yankunan biyu ba.
Motoci bakwai dauke da mai da iskar gas sun shiga yankin Zirin Gaza ta kan iyakar Rafah, kamar yadda Wael Abu Mohsen, shugaban sadarwa na bangaren Falasdinawa ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu.
0230 GMT — Isra'ila ta kama Falasdinawa 3,390 a Yammacin Kogin Jordan tun ranar 7 ga Oktoba
Sojojin Isra'ila sun tsare Falasdinawa 3,390 a hare-haren da suka kai a yankin Yammacin Kogin Jordan da suka mamaye tun ranar 7 ga watan Oktoba, ciki har da 260 din da aka kama a lokacin da aka tsagaita wuta, in ji kungiyoyi masu zaman kansu na cikin gida.
A cikin wata sanarwar hadin gwiwa da kungiyar fursunoni ta Falasdinu da hukumar kula da fursunonin suka fitar, ta ce an kama mutanen ne a cikin gida da kuma wuraren binciken sojoji da suka hada da wadanda aka tilasta musu miƙa wuya sakamakon matsin lamba da kuma wadanda aka yi garkuwa da su.
A ranar Alhamis ne aka kama mutum 30, yayin da adadin wadanda aka kama a ranar Laraba zuwa daren Alhamis ya kai 40, in ji su.
0146 GMT — Wani ɗan Isra'ila da ke tsare a hannun Hamas ya roƙi Netanyahu ya kwaso gawarwakin iyalinsa daga Gaza
Wani ɗan Isra'ilan da ke tsare a hannun ƙungiyar Hamas ya roƙi Firaminista Benjamin Netanyahu ya tsara yadda za a kwaso gawarwakin iyalinsa daga Gaza tare da yi musu jana'iza a Isra'ila, bayan da suka mutu a wani harin sama na Isra'ilan da ta kai yankin Gaza da ta yi wa ƙawanya a lokacin da suke tsare a wajen Hamas.
Roƙon ya zo ne a cikin wani saƙon bidiyo da rundunar Qassam ta Hamas masu dauke da makamai, ta fitar.
“Bibi [Netanyahu], kun jefa bam tare da kashe matata da ’ya’yana biyu, wadanda su ne abu mafi muhimmanci a rayuwata,” in ji Yardin Bibas.
"Ina roƙonka ka mayar da iyalina zuwa ƙasarsu domin a binne su a Isra'ila, "in ji shi cikin yanayi na tausayi.
“Bibi, ina roƙonka ka mayar da su Isra’ila, don Allah ka dawo da su gida.