Lugude: Mutumin da ke wallafa tsofaffin hotunan arewacin Nijeriya
Daya daga fitattun masu wallafa tsofaffin hotunan tarihi na Nijeriya musamman ma na arewa a shafukan sada zumunta Buhari Sale Abubakar, da aka fi sani da Lugude ya bayyana in da yake samun hotunan da yake wallafawa da hotunan da suka fi jan hankalin masu bin shafinsa.