Kantin Kwari: Kasuwar tufafi mafi girma a Yammacin Afirka
Kasuwar Kantin Kwari da ke birnin Kano na Arewacin Nijeriya, wadda aka kafa a shekarun 1930, ita ce kasuwar tufafi mafi girma a Yammacin Afirka, inda take taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa tattalin yankin.
Dubban mutane daga ciki da wajen Nijeriya suna zuwa kasuwar domin gudanar da harkokin kasuwanci, kamar yadda za ku gani a wannan rahoto na musamman da Yusuf Ibrahim Yakasai ya haɗa mana, yayin da ya ziyarci kasuwa.