Iyayen daliban Kaduna sun nemi a kubutar da 'ya'yansu
Iyayen ɗaliban firamaren da ƴan fashi suka sace a makarantarsu a garin Kuriga na Jihar Kaduna a makon da ya wuce, sun ce suna cikin matuƙar tashin hankali na rashin tabbas na halin da ƴaƴansu ke ciki, kuma sun ƙagara a gano yaran, waɗanda ba a san a halin da suke ciki ba
Tuni dai rundunar sojin Nijeriya ta ce dakarunta sun bazama neman yaran.