Hanyar Abuja-Kaduna: Lalacewar hanya mafi muhimmanci a arewacin Nijeriya
Hanyar Abuja zuwa Kaduna hanya ce mai matukar muhimmanci a Nijeriya inda dubban motoci ke bin hanyar a kullum. Ana yawan samun hatsarin mota a hanyar da cunkoson ababen hawa sakamakon yadda hanyar ta lalace duk da cewa an shafe tsawon shekaru ana gyaran hanyar amma ba a kammala ba.