Daɗaɗɗiyar kasuwar kwaɗi a Arewacin Nijeriya

Daɗaɗɗiyar kasuwar kwaɗi a Arewacin Nijeriya

Kasuwar sayar da kwaɗi da ke Jihar Kano na daga cikin kasuwannin da suka shahara wurin sayar da kwaɗi a Nijeriya. Sakamakon yadda kasuwancin kwaɗi ke bunƙasa, masu sana’ar a kasuwar kwaɗi ta Na’ibawa na biyan haraji ga gwamnati kamar sauran ‘yan kasuwa kuma gwamnatin na amfani da kuɗaɗen wurin aiwatar da ayyukan more rayuwa.