Boko Haram: Halin da ‘yan gudun hijirar Nijeriya suke ciki a ƙasar Chadi
Wasu daga cikin ‘yan gudun hijirar Nijeriya da ke Chadi sun shaida wa TRT Afrika Hausa irin mummunan halin da suka shiga bayan mayaƙan Boko Haram sun tilasta musu yin hijira.Sun bayyana cewa akwai lokacin da suka taɓa shafe watanni 11 ba su samu tallafin ko da kwano ɗaya na abinci ba.