Yarinya Bafalasdiniya Eman Al-Kholi kwance a asibiti bayan an yanke mata kafa saboda raunin da ta samu a harin da Isra'ila ta kai wa idansu inda iyayenta duk sun mutu, na kwance a asibiti da ke Rafah, kudancin Gaza. / Hoto: Reuters

Daga Miranda Cleland

Watanni tara na kisan kiyashi a Gaza, ana ci gaba da yi kuma, akwai dubban yaran Falasdinawa da ke rayuwa da wani bangare nasu da aka yanke inda suke ci gaba da samun kula wa a asibitoci.

Dr. Hassan Ghassan Abu Sittah, mai aikin tiyata dan kasar Birtaniya kuma Bafalasdine da ya yi tiyata ga Falasdinawa da dama da suka raunata a Gaza, ya yi hasahen a yanzu haka akwai mutum 5,000 aka yanke wa kafa.

Hakan ya ƙaru sosai idan aka kwatanta da karshen shekarar da ta gabata, lokacin tilas ta sa aka yanke wa yaran Falasdinawa 1,000 ƙafafu.

Fiye da watanni bakwai kenan da wannan kiyasi na farko, kuma yakin da Isra'ila ke yi na kisan kare dangi bai nuna alamun zai ƙare ba.

"Wannan ne babban intila'i na yanke kafafuwan yara a tarihi", in ji Abi Sittah a wajen wani taro, yayin da Isra'ila kuma ke ci gaba da kai wa Falasdinawa hari a Gaza ta sama da ta ƙasa da ruwa, akwai wahalar isar da kayan taimako zuwa yankin, ballantana bai wa likitoci damar zuwa kula da yaran da aka jikkata.

An kai wa wata yarinya 'yar Gaza mai shekara hudu da iyalinta hari a lokacin da suke kokarin guduwa bayan Isra'ila ta kai wani hari ta sama a kudancin Gaza a watan Nuwamban 2023.

"Tankar yaƙin ta sanya 'yata ta rasa kafarta," in ji mahaifiyar Ghazal a yayin tattaunawa da mai bincike na Kungiyar Tsaron Yara Duniya da na Falasdinu (DCIP), inda na ke aiki a matsayin a matsayin mai jami'in tsare-tsare a Washington DC.

"Likitoci dole suka yanke ƙafarta ba tare da allurar kashe zafi ba. Akwai wasu wuƙaƙe a wajen. Sun kai tukunyar Gas don gasa wuƙaƙen, sai suka fara yanke kafar. "'Yata tana ihu."

Radadin da ba a taɓa tunani ba

Ba Ghazal ce kadai a cikin radadin ba. Akwai wasu da dama a Gaza da aka yanke wa wasu gaɓɓai nasu a cikin awanni da yawa kuma ba tare da yi musu allurar kashe zafi ba - zafi da radadin da ba a taba tunanin samun sa ba ga yara kanana.

Likitoci da ma'aikatan lafiya na yanke kafafun yara kanana a asibitocin da jama'a suka yi yawa inda dubban Falasdinawan da aka tsugunar suke neman mafaka a cikin duhu, inda dakunan tiyata ma ba sa samun lantarki, babu magunguna kashe radadi, babu antibiotics, inda Isra'ila kuma ke ci gaba da kai hare-hare.

Hare-Hare da kisan kiyashin isra'ila sun gurgunta tsarin kula da lafiya a Gaza. Babu wani bin diddigin marasa lafiya ko duba su sosai. Kuma babu kayan magani gaba daya da kafafuwan katako.

Yaron da aka yanke wa kafa yake tafiya da taimakon kafar katako, na bukatar sabuwa tun shekarar da ta gabata, a wasu lokutan kuma suna bukatar su sosai, duba ga girman yaran.

Yaran da ake yanke wa kafa a Gaza na iya fuskantar karin matsaloli, a loakcin da suke yin jinya, suna shan tsananin zafi, kamuwa da wasu cututtuka da karuwar ranukan buraguzan bam din da ke fashe wa.

Ritaj mai shekara takwas, matashiyar Falasdin da ta fito daga yankin Juhr Al-Deek, kudancin Gaza, ta tsira daga harin bam din Isra'ila d aya hallaka iyalinta.

Bayan kwanaki biyu a akrkashin buraguzan gini, an kubutar da Ritaj.

Ta dole likitoci suka yanke mata kafarta guda daya bayan aikin tiyata, inda a yanzu take gwagwarmayar warkewa a sansanin 'yan gudun hijira da UNRWA suka samar.

"Likitan ya duba kafata, sai ga tsutsotsi na zubowa daga ciki" Ritaj ta fada wa mai nincike na DCIP wanda ya ziyarci makarantar UNRWA inda take jiyya da goggonta.

"A kowace rana, ba na iya bacci saboda karar hare-haren bam kuma ina son yin bacci saboda tsananin zafin da na ke ji a kafata, amma haka na ke jurewa."

A yayin da wasu yaran Falasdinawa da aka jikata suke nan da kafafunsu, wasu da dama na fuskantar mutuwar wani bangare na jikinsu da ma wasu matsaloli tare da hakan.

Labarin me ya samu Mohammed

Yakin na ta jikkata yara kanana da ke Gaza.

Wani jirgin harbi na Isra'ila ya harba harsashai da suka samu Mohammed dan shekara 15 a baya a lokacinda yake tafiyaa titin Salahaddin na garin Gaza a tsakiyar watan Maris, kamar yadda bayanan da DCIP suka tattara suka nuna.

Mohammad ya dinga zubar da jini tsawon awanni biyu a kasa kafin Falasdinawa da suka zo wuce wa su gan shi su kai shi asibitin Al=Ahli. Jim kadan bayan hakan, aka mayar da shi Asbitin Kamal Adwan, inda aka yi masa tiyata

A yanzu, Mohammad ya samu mutuwar rabin jiki daga kugunsa zuwa kasa, ba ya iya amfani da kafafuwansa.

A baya ina kaunar wasa da abokaina, wadanda na rasa wasu daga ciki a yakin da ake yi, amma yanzu ba zan iya wasa ba saboda ciwo," in ji Mohammad yayin ganawa da DCIP. "Na kasance mai kaunar wasan kwallon kafa, ina zama mai tsaron gida."

Kafin Oktoba, yaron Bafalasdine dan shekara 16 ya shaida hare-hare munana na Isra'ila a Gaza da ya yi ajali da jikkata daruruwan mutane.

A yau babu wani yaro a Gaza da bai dimauta ba, wanda ake iya gani karara ta hanyar bayyana damuwa, tunanin kashe kai, fitsari a kwance, rikicewar tunani, ta'addanci da tsakar dare da ma wasun su.

Kimanin kashi 12 na yaran Falasdinawa da ke Gaza sun fuskanci wani nau'i na "wahalar motsi da jiki" kafin ma a fara wannan yaki na Gaza, kamar yadda UNICEF ta bayyana.

Ko yaro mai lalura a jiki ko a ƙwaƙwalwa, suna fuskantar hatsari sakamakon hare-haren Isra'ila.

Yara kanana da ke amfani da keken guragu ko wasu abubuwan taimakawa a yi tafiya da matsawa, ba za su iya zuwa ko ina cikin sauki ba a tsakanin rusassun gine-gine.

Jama'a masu rauni

Akwai yarinya mai suna Dunia mai shekara 12 da ta tsira a harin Isra'ila d aya hallaka iyayenta da 'yan uwanta da kuma yanke kafafunta.

"Jini ya zuba sosai kuma ba ni da kafa," Duniya ta fada wa masu bincike na DCIP a watan Nuwamba. "Na yi kokarin motsa kasar, amma ba ta motsa wa."

Hare-Haren Isra'ila ne suka tsugunar da Dunia, kuma gine-gine sun danne iyayenta, wanda hakan ya sanya ta zama maraiiniya, kuma kafarta ta bar jikinta.

A yayin da Duniya ke farfadowa a asibitin Naser da ke Khan Younus, a watan Disamban 2023 wata tankar Isra'ila ta kai hari asibitin inda skaamakon haka ta rasa ranta nan take.

Dakarun isra'ila na aikata ta'annati kan yaran Falasdinawa da ke Gaza a koyaushe. a yayinda yaran d ake mutuwa a Gaz ake daduwa har suka haura 15,000, wasu yaran da dama sun fukanci raunuka sakamakon hare-haren na Isra'ila.

Dole ne kasashe su dakatar da kai makamai ga sojojin isra'ila saboda yara kanana da ke Gaza na bukatar tsagaita wuta a yau,.

Yaran Falasdinawa da aka nakasta na bukatar warkewa daga ciwukansu - damar da dakarun isra'ila suka kwace daga wajen Dunia.

Matsayin doka

Ga yaran Falasdinawa da aka nakasta irin su Ghazal, Ritaj, Mohammad da dubunnai da suka samu raunuka a yanzu suna motsi a duniya ba tare da wani bangare na jikinsu ba, ya kamata a tabbatar da yaran nan sun samu kulawa, ilimi da sake gina rayuwarsu, ba wai hakkinsu ba ne kawai, mataki ne da doka ta tanada.

Isra'ila ta sanya hannu kan Yarjejeniyar Kare Hakkin Yara ta Majalisar Dinkin Duniya a 1991, inda ta yarda da za ta kare hakkokin yara.

Sashe na 23 na yarjejeniyar ya mayar da hankali kan hakkokin yara na musamman da ma nakasassu.

Ya kamata su samu kulawa da ilimi na musamman don mayar da su ga cikin al'umma, da kuma hakkinsa na samun ilimi, horo da kula da lafiya.

Kisan kiyashn Isra'ila a Gaza na nufar yara kanana da aka nakasta wadanda ba za su iya gujewa hare-haren da ake kai wa ta sama ba, suna jin karar harbe-harbe da musayar wuta.

Bayan watanni tara na kisan kiyashi a Gaza, yaran Falasdinawa na fama da matsalolin lafiya masu rikitarwa, kuma ya rage na hukumomin kasa da kasa na su sanya dokar hana kai makamai ga Isra'ila, sannan su tuhumi shiugabannin Isra'ila da laifukan yaki.

Miranda Cleland jami'ar tsare-tsare ce a kungiyar kare yara kananan Falasdinawa ta 'efense for Children International - Palestine and lives'. ta yi digirinta na farko a fannin nazarin kasa da kasa da harshen Larabci a Jami'ar Amurka

Togaciya: Ba dole ba ne ra'ayin marubucin ya zama daidai da ra'ayi ko dolokin aikin jarida na TRT Afrika ba.

TRT Afrika