Daga Hannan Hussain
Donald Trump yana fama da kalubale da dama a shirinsa na sake yin takarar Shugaban Kasa. Tsohon Shugaban Kasar yana fuskantar matsalolin shari'o'i da dama da suka kunshi almundahana da bayar da kudade domin a tafka magudin zabe.
Trump yana fuskantar kusan shari'o'i guda 19 a jihohi biyu da gundumomi biyu a kasar. Duk da ya samu rinjaye a zabukan gwaji, amma har yanzu yana fuskantar barazanar tafiya gidan kaso.
Shari'o'in na Trump ya jawo hankalin kafafen sadarwa sosai. A watan jiya aka gabatar da shi a kotu a New York.
Ana zarginsa ne da bayar da bayanan karya na harkokin kasuwancinsa da kuma biyan kudi domin a yi magudin zabe, wanda ake zargin ya ba jarumin finafinai batsa, Stormy Daniels kafin zaben Shugaban Kasa na 2016, kuma za a kammala shari'ar ce jim kadan da zabe.
Haka kuma yana fuskantar wasu tuhume-tuhumen da suka hada da samun shi da wasu takardun gwamnati ba bisa ka'ida ba. Da kuma kin ba FBI goyon bayan karbo takardun, da kuma cewa shi bai da laifi.
Sai dai da duk da wadannan matsalolin da yake fuskanta, akwai alamu da suke nuna Trump zai tsallake su.
Cacar shiga zabe
Maimakon fuskantar kowace tuhuma a kotu ita kadai, sai Trump ya zabi ya ja shari'o'in har bayan zaben na Nuwamba.
Wasu zabukan gwaji da aka yi na kwana-kwanan nan suna nuna cewa Trump zai iya samun nasara a zaben mai zuwa. Idan kuwa ya samu nasara, zai iya bata shari'ar ta hanyar nada wadanda yake so a sashen shari'ar kasar.
Kuma da alama wannan jan kafar da yake yi yana samun nasara lalata shari'o'in guda biyu: Na biyan kudi a yi magudi da mallakar wasu takardun gwamnati.
Jan kafar kuma na kara taimakon Trump wajen kare shi daga fuskantar wasu tuhume-tuhumen. Ya sha bayyana cewa idan ya samu nasara a zaben, zai yafe wa wadanda aka kama da laifin zanga-zanga a Fadar Gwamnatin Amurka.
Hakan kuma zai sa shi ma ya samu sauki a game da tuhume-tuhumen da ake masa da suka danganci zabe. Daga cikin tsarin jan kafar akwai kokarin jawo abokan siyasarsa da masoyansa kusa da shi domin su tausaya masa.
Wannan hanyar da ya bi ta fara ba shi nasara. A Jihar Florida, wani alkali wanda shi Trump din ne ya nada shi a zamanin mulkinsa ya dage wani zaman shari'a da za a yi. Wannan yana cikin cikin dage-dagen da aka yi da ke amfanar Trump din da masoyansa.
Zai yi wahalar gaske a ce Trump ya bayyana kowane zaman kotun domin fuskantar tuhume-tuhumen da ake masa. Maimakon haka, sai ya zabi caccakar tsarin da ake bi wajen tuhumarsa din domin jan shari'o'in har zuwa bayan Nuwamba. Wannan shi ne babban burin lauyoyinsa.
Batun siyasa
Trump na da burin ganin shari'o'in da yake fuskanta sun kai har zuwa Nuwamba. Daya daga cikin hanyoyin da yake bi shi ne ya nuna wa duniya cewa bita-da-kulli ake masa.
Trump yana so ya yi amfani da wannan tsarin ne domin masu zabe su tausaya masa. Idan ba a manta ba, ya yi zargin an tafka magudin zabe a zaben 2020, sannan an zarge shi da hassala mutane domin gudanar da zanga-zanga a Fadar Gwamnatin Amurka, wanda aka so a yi amfani da shi a tsige shi. Shi dai Trump yana cigaba da nuna cewa duk bita-da-kulli ake masa.
Yadda abin yake a yanzu shi ne: Mutanen kasar da dama sun gaji da Shugaba Biden, sannan Trump yana da rinjayen masoya a manyan jihohi guda biyar duk da matsalolin tuhume-tuhumen da yake fuskanta. Ganin yadda yake da alamar samun nasara, me zai hana Trump gwada sa'arsa wajen shiga zaben?
Haka kuma mutanensa na Jam'iyyar Republican suna tare da shi. Manyan jagororin jam'iyyar sun nuna masa goyon baya, sannan jagoran 'yan Republican a Majalisar Wakilan kasar, Mike Johnson ya nuna yana tare da Trump sosai.
"A zahiri yake cewa bangaren shari'ar kasarmu ya zama 'yan amshin shata domin bata sunan Trump," inji Johnson.
Ganin yadda tsohon Shugaban Kasar yake samun karbuwa a tsakanin mutane da ma a cikin jam'iyyarsa ne yake kara jawo wasu 'yan jam'iyyar Republican din suke cigaba da kare shi.
Trump na da karfi sosai a Majalisar Wakilan kasar, wanda hakan ya sa yake da ikon fada a ji. Yadda Trump ya taimaka wa Johnson wajen tsallake yunkurin tsige shi daga Shugaban Majalisar alama ce ta karfin da yake da shi a majalisar.
Matsalolin da suka faru a zabe
Trump zai iya fuskantar zaman gidan yari idan ya cigaba da magana ko zargin magudin zabe. Idan hakan ya faru zai kawo tsaiko babba ga 'yan Republican wadanda suke so su yi amfani da wannan fafutikar ta Trump domin sa shakku a kan zaben na bana.
Wata matsalar ita ce zanga-zangar da aka yi a Fadan Gwamnatin Amurka, wanda ba karamin abin kunya ba ce ga kasar. Amma ta hanyar cigaba da nuna adawarsu da yanayin shari'o'in, magoya bayan Trump za su iya kara samun masoya su rika tausaya masa domin samun kuri'unsu a zaben mai zuwa.
Wani abun kuma shi ne babu wata matsala idan suu 'yan Republican son sun yi zargin magudin zaben a madadinsa.
Wannan ya sa ake tunanin ya daina maganar, sai ya bukaci su cigaba da bayyana wa duniya, inda suke caccakar Michael Cohen wanda tsohon na hannun daman Trump din ne wanda ya bayyana a gaban kotu cewa Trump ya sa ya ba da kudin magudin zabe.
Ta hanyar diga alamar tambaya a kan Cohen, Trump zai iya kawo tsaiko a kan shari'o'in sannan ya nuna cewa bita-da-kulli ake domin siyasa.
Don haka sakon a bayyana yake, babban burin Trump shi ne ya nuna wa masoyansa cewa tuhume-tuhumen da ake masa siyasa ce kawai.
Domin samun nasarar haka kuwa, zai yi duk mai yiwuwa domin jan shari'o'in nan har zuwa Nuwamba.
Lallai hakan idan ya yiwu zai zo wa Amurka da wani yanayi na daban. Trump ne Shugaban Kasa na farko da ya taba fuskantar tuhume-tuhume haka, sannan gabatar da shi, (da kuma watakila darewa) zai iya nuna cewa lallai ashe babu wanda ya fi karfin doka a kasar.
Amma yadda yake jan kafa a shari'o'in ya nuna cewa akwai hanyoyin da za a iya bi a tsallake tuhume-tuhumen, duk kuwa da yadda tuhume-tuhumen suka bayyana a zahiri.
Ganin yadda alamun daure shi ke kara samun tsaiko ne ya sa wasu suke saka alamar tambaya a kan bangaren shari'a da dimokuradiyyar Amurkar baki daya.
Game da marubucin: Hannan Hussain babban mai sharhi ne a kan harkokin yau da kullum na duniya. Yana bincike a kan abubuwan da suka shafi tsaro da sulhu da alaka tsakanin kasashen yankin Gabas ta Tsakiya da Asia. Ya taba yin aikin a matsayin mai a Cibiyar Policy Research Institute (IPRI), sannan ya yi rubuce-rubuce a Mujallar Carnegie Endowment for International Peace da Mujallar Georgetown Journal of International Affairs, da Mujallar Express Tribune (wadda take aiki tare da Mujallar New York Times).
Togaciya: Ba dole ba ne ra'ayin marubucin ya zama ya yi daidai da ra'ayi ko ka'idojin aikin jarida na TRT Afrika.