Daga Farfesa Abdallah Uba Adamu
Watakila a karon farko a fara tunanin ko masana’antar fina-finan Hausa ba ta da alaka da masana’antar fina-finan Indiya ta Bollywood da ita ce ta biyu bayan Hollywood ta Amurka a wajen karfi da yaduwa a duniya.
Gaskiyar zance shi ne, Kannywood, sunan da masana’antar finan-finan Hausa ta zaba wa kanta ya samo asali ne daga Bollywood a lokacin da wani marubuci Sunusi Shehu Burhan ya yi rubutu a mujallar Tauraruwa ta Hausa wadda aka wallafa a watan Agustan 1999.
Duk da rashin yaduwa sosai na masana’antar fina-finan Hausa a wasu sassan duniya, wannan lakanta suna shi ne irin sa na farko a tsakanin masana’antun fina-finai na Afirka.
Ana danganta kirkirar sunan Nollywood ko masana’antar fina-finan Nijeriya ga Norimitsu Onishi na jaridar New York Times a 2002, wanda hakan ke nufin shirya fina-finai a Nijeriya duk da bambance-bambancen al’adu da ke tsakanin jama’ar kasar.
Watakila wannan na yin bayani game da masana’antun fina-finan harsunan cikin gida na Nijeriya da ba sa cikin ‘Nollywood’.
Fina-finan Nollywood sun taikata ga na Turanci ne kawai (Genevieve Nnaji, Daraktar fim din Lionheart, ta yi mamakin yadda aka ki karbar shirin don shiga gasar Oscar saboda amfani da harshen Turanci).
Duk da haka ba za a dauki Nollywoood a matsayin masana’antar fina-finan Nijeriya da ke wakiltar kowanne bangare ba, kamar yadda su ma ‘yan Nijeriya suke, za su bayyana yadda suka fito daga bangrori daban-daban.
Duk kokarin da aka yi na sanya sauran fina-finan Nijeriya da ake yi a harsunan gida a karkashin Nollywood ya ci tura.
Fina-finan sauran harsunan Nijeriya na cikin gida ba su ta’allaka ga al’amuran da suke faruwa bayan mulkin mallaka ba—wanda wannan ne daya daga cikin kashin bayan fina-finan Nollywood.
Duba zuwa ga masana’antar Woods
To mene ne zai zama ginshikin fim a Kannywood? A bayyane yake karara babu wani daga cikin maudu'ai da ake da su da zai yi dadai da na fina-finan Yamma.
Tabbas an yi rubuce-rubuce da dama a kan yadda ake bayyana mace a fina-finan Hausa (ana amfani da salo mai kare mata), amma babu wani da aka mika don a duba shi wanda yake ginuwa kan tsarin Marxist, Queer ko Auteur.
Mafi yawan nazari da rubuce-rubucen da aka yi a litattafai da mujallu, da wadanda aka gabatar a wajen manyan tarurrukan fina-finan Hausa, suna bayani ne kan ginshikai da ke warwara kan gabobin al’adu a addinin da ake bayyanawa a fina-finan Hausa, sabanin abin da nake kira “Matattarar bayanan bai-daya”.
Amma tukunna ma waye ya ce dole sai mun samu maudu'i? Idan zan yi bayani kan abin da Michael Chekhov ya fada, shin ba salo ba ne?
Ku san dukkan fina-finan Kannywood na dauke sako guda uku: labaran soyayya, rikicin cikin gida na iyali da kuma rawa, kida da waka, duk da cewa a tsawon shekaru rawa da wakar sun ragu sosai.
Kamar yadda masu shirya fina-finai da dama suka ambata ne, babu tantama Bollywood ne ke yin tasiri a kan hakan.
Maudu'in Kannywood ya fado cikin karamin ajin Bollywood na fina-finai gama-gari. Har ya zuwa 2007, harshe ne kadai ya bambanta fina-finan Kannywood da na Bollywood, wanda bayan wannan lokacin ne aka samu sabbin abubuwa da aka karawa fina-finan Hausa.
Da fari dai, abin ya zama tsantsar bayani kan kabila. Ba wai batu ne na cakuda wasu abubuwa ba ko kuma “Wood”, sai dai kawai bayanin rayuwa a biranen Hausawa da al’adun birni.
Yadda fina-finan Hausa suka samu nasarar cika Youtube na tabbatar da wannan magana.
Abu na biyu kuma shi ne, abin ya zama mai tabo kabilu daban-daban – ana bayar da labaran kabilu a matsayin abin da ake bukatar don zama lafiya tare.
Dadin Kowa, wani gari a arewacin Nijeriya da ya dabbaka irin wannan gamayya.
Abu na uku kuma, ana kallon fina-finan a fadin duniya – ta yadda abun ya yadu a kasashe masu magana da yaren Turanci da Faransanci da ke Afirka matukar dai akwai jama’ar Hausa a wajen ko yaya suke kuwa.
Na hudu kuma shi ne yadda kalmar Kannywood ta yi shekaru 24 tana tashe. Lokaci ne a kawar da ita.
Su kansu masu shirya fina-finan da jaruman na fadin haka.
Shaidar hakan shi ne bayyanar Kaddywood a Kaduna, don kalubalantar Kannywood na Kano – ba wai sun zama masana’antun fim ba, kenan sun koma kungiyoyin da ke kokarin biyan bukatunsu, neman suna da kuma samun riba mai yawa ta hanyar haduwa da ‘yan siyasa da jami’an gwamnati.
Babu wani mai zancen maudu'i ko yadda za a siffanta wani ko wata.
Abu na karshe kuma mafi muhimmanci shi ne, a yanzu kalmar ba ta da wata alaka da garin Kano – kamar yadda (Bollywood yake daga Bombay ko Nollywood daga Nijeriya).
Ghana, Kamaru da Nijar ma a yanzu sun zama wuraren samar da finan-finan Hausa sosai, rarraba su da kallon su, ba tare da sai an kawo su Kano ba don tantance su ko sayar da su ba. Sunansu fina-finan Hausa, ba fina-finan Kannywood ba.
Tun da dai babu “tsarin samar da fina-finai na Kannywood”, zai zama rashin azanci a ci gaba da kiran fina-finan da aka samar da Hausa a matsayin na Kannywood.
Su kansu masu shiryawa da kallon su suna kiran su da fina-finan Hausa. Masana’antar fina-finan Hausa ita ce ma’anar fina-finan.
Na tabbata akwai wasu gabobi da dama da mutane za su iya karawa a nan. A saboda hakan zan bayar da shawarar amfani da ‘Masana’antar Fina-Finan Hausa’ a madadin Kannywood.
Wannan zai sanya masana’antar ta zama mai wakilta ko bayyana al’adu da yanayin rayuwar Hausa a duk inda suke.
(Marubucin wannan makala Malami ne a Jami’ar Bayero da ke Kano, Nijeriya).