An baje tutar nuna adawa da Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu, yayin da a gefe guda wata mata ce ke rike da tutar Isra'ila kusa da 'yan sanda, a ranar zanga-zangar adawa da gwamnatin Netanyahu, a birnin Tel Aviv na kasar , Maris 9, 2024 (Reuters/Carlos Garcia Rawlins) . / Hoto: Reuters   

Daga Hamzah Rifaat

Lokaci ya yi da za a sake kafa gwamnatin Isra’ila da kuma gudanar da sabon zaɓe, domin a yanzu Firaiminista Benjamin Netanyahu ya zama “babbar matsala” ga zaman lafiyar yankin Gabas ta Tsakiya.

Waɗannan kalamai masu -jan hankali- sun fito ne daga shugaban masu rinjaye na Majalisar Dattawan Amurka Chuck Schumer, Bayahuden Ba'amurke mai babban matsayi a gwamnatin ƙasar.

Kalaman nasa na zuwa ne a daidai lokacin da kiraye-kirayen a gudanar da zaɓe a Isra'ila ke daɗa ƙamari a Amurka da kuma ita kanta Isra'ila.

Sai dai, Netanyahu ya yi watsi da kiraye-kirayen a gudanar da zaɓen da wuri, kana ya mayar da mummunan martani ga sukar Schumer, yana mai cewa Isra’ila ba ‘jamhuriyar ''da ba a bin doka' ba ce.

To amma, tafiyar Netanyahu za ta sauya manufofin Isra'ila kan Gaza?

Maganar gaskiya ita ce, farin-jinin Netanyahu yana raguwa a gida da waje. Alamun hakan shi ne, Washington da Ottawa suna tattaunawa da mamban majalisar ministocin Isra'ila Benny Gantz kana abokin hamayyar Netanyahu.

Samun wannan amsar za ta buƙaci yin nazari sosai kan abin da ke faruwa a cikin Isra'ila.

A bayyane yake cewa, akasarin jama'a sun juya baya ga Netanyahu, yayin da kashi 15 cikin 100 na ƴan Isra'ila ke nuna sha'awarsu kan ya ci gaba da kasancewa a kan karagar mulki bayan kawo ƙarshen yaƙin da ake kan yi.

Sai dai kuma, mabiya ɗarikar Orthodox masu tsattsauran ra'ayi da jam'iyyu masu ra'ayin kishin ƙasa da ke ƙawance da jam'iyyar Likud sun samu gagarumar nasara a zaɓukan ƙananan hukumomi da aka gudanar kwanan nan cikin shekarar 2024.

Har ilau, jam'iyyun da aka fi sani da masu ra'ayin gurguzu irin su Meretz tare da babban shugabansu Yair Golan sun yi kira da a yi wa Falasɗinawa kisan kiyashi a Gaza tare da ɗaukar makaman yunwa a wani yunƙuri na farfaɗo da burinsu na siyasa.

Duk da cewa nasarorin da jam'iyyar Likud da ƙawayenta suka samu a matakin kananan hukumomi ba su nuna ainihin abin da ke faruwa a matakin kasar ba.

A zahiri dai, ba tare da la'akari da wanda ke kan mulki ba, manufofin Isra'ila kan Gaza ba za su sauya ba.

Idan aka yi hasashe kan ministan Isra'ila Benny Gantz wanda ke kan gaba a zabukan kananan hukumomi da aka gudanar gabanin babban zaben kasar da Netanyahu ya ki bari a yi. Dubban masu zanga-zanga a Tel Aviv sun bukaci Gantz ya yi watsi da kawancen Netanyahu tare da janye goyon bayansa ga Firaiministan.

Bisa ga kuri'ar jin ra'ayin da Cibiyar Bincike ta Lazar ta samar wa jaridar Isra'ila Maariv, kashi 49 cikin 100 na wadanda suka amsa tambayoyin binciken sun nuna amincewarsu ga Gantz a matsayin shugaban jam'iyyar Hadin kai ta kasa da kuma matsayin firaminista mai jiran gado.

Sai kuma kashi 28 cikin 100 ne kawai suka amince Netanyahu ya ci gaba da rike mukaminsa.

Ziyarar Gantz zuwa kasar Kanada da Amurka akai-akai tare da irin tarba mai kyau daga kasashen a maimakon Netanyahu, ya nuna karara cewa shi ne ɗan takarar da kasashen yamma suka fi so a tsakaninsu.

Sai dai abin da hakan ke nufi a nan shi ne: Ficewar Netanyahu da zuwan Gantz ba zai magance matsalolin Falasdinu ba - sai dai ya tsawaita shi. Gantz ba mai son zaman lafiya ba ne.

Yana wakiltar wani bangare na siyasar Isra'ila wanda ke kira kan a kiyaye tare da mutumta matsayin da ake kai a yanzu.

Hakan ya hada da karfafa haramtacciyar matsugunan Isra'ila a yankin Yammacin Kogin Jordan da ta mamaye, inda aka shata kogin Jordan a matsayin iyakar Isra'ila, yanayin da ke kara inganta kawancenta da Amurka don cin gajiyar gudummawar Amurkan na shekara-shekara da ya kai dala biliyan 3.8 kan kasafin kudin sojin Isra'ila da kuma ci gaba da kisan kare dangi a Gaza.

Ana iya kwatanta Gantz a wasu da'irorin a matsayin mutum mai matsakaicin ra'ayi a majalisar ministocin Isra'ila, amma duk da haka akidarsa tana kama da na Netanyahu.

Wannan ita ce gaskiyar da gwamnatin shugaban Amurka Joe Biden ta kasa ganewa.

Zaɓin Washington na yin hulɗa da Gantz maimakon Netanyahu ba zai iya kawar da gaskiyar batun warware rikicin wanda ya ta'allaka wajen ba da himma tare da aiwatar da mulkin Falasɗinawa da kawo ƙarshe da kuma soke mamayar matsugunai da kuma ba wa Falasɗinawa yancin komawa yankunansu.

Duk da cewa yana iya zama mai hikima da zai iya maye gurbin Netanyahu, Gantz yana haɓaka manufofin rashin samar da zaman lafiya wanda ya saɓa da yanayin da ake ciki a Gaza.

Kazalika jami'an gwamnatin Biden sun yarda da cewa ganawar da aka yi Gantz ya haifar da tattaunawa masu tsauri, inda ministan ya bayyana aniyar kasar na kin amincewa ta takaita kai hare-hare Rafah da kuma kayayyakin agaji.

Hakan ya nuna matakin da Washington ta bi wajen tuntubar abokin hamayyar Netanyahu a matsayin wanda ya cancanta, tare da mumunta taimakon soji da kuma tabbatar da goyon da take baiwa Isra'ila yana nan inda ya ke.

Rashin amincewar Biden kan dakatar da taimakon soji yayin da yake kokarin rage karfin Netanyahu, na zuwa ne adaidai lokacin da kashi 52 cikin 100 na Amurkawa suka ki ba da amincewarsu kan Amurka ta aika makamai zuwa Isra’ila har sai ta daina kai hare-hare Gaza.

Bayan Gantz akwai wasu abubuwan da ke faruwa a Isra'ila waɗanda za su iya ƙarfafa halin da ake ciki ba tare da la'akari da tafiyar Netanyahu ba.

A cewar wani kuri'ar jin ra'ayin jama'a daga Cibiyar Dimokradiyyar Isra'ila, Jam'iyyar Power Party karkashin jagorancin ministan tsaron kasar Itamar Ben Gvir za ta kasance jam'iyya daya tilo daga cikin abokan kawancen gwamnati da za ta yi nasara wajen tabbatar da kasancewarta a zaben.

A bayyane yake cewa tafiyar Netanyahu kamar yadda Chuck Schumer ya yi kira a kai ba zai canza manufofin Isra'ila a kan Gaza ba.

Matsalar dai ta ta'allaka ne kan yanayin kasar Isra'ila, da manufofinta na siyasa da kuma ci gaba da take hakkin Falasdinawa.

A taƙaice, ficewar Netanyahu ba zai magance matsalar Falasɗinawa ba.

TRT Afrika