Yunkurin Pan-Africanism ya bayyana ne a karshen karni na 19 da farkon karni na 20./ Hoto: Getty  

Daga Dwomoh-Doyen Benjamin

A yanayi irin na bambance-bambance dan'adam, a mafi yawan lokuta batun sanin asali kan fadada zuwa iyakokin kasa da al'adu da kuma gado na tarihi.

A cikinsu duka, Akidar Pan-Africanism ce ke jagorantar wadannan ka'idoji, ba kawai ana nufin tsantsar magana ba, amma samun ainihin asali da ya ƙunshi tushe da gwagwarmaya da muradun jama'a daban-daban masu alaka iri daya wadanda ke warwatse a nahiyoyin duniya.

Abu muhimmi shi ne, akidar Pan-Africanism ta zarce iyakokin yankin Afirka kawai, ta hada dukkan mutanen da suka fito daga Afirka, walau suna tsakiyar nahiyar ne ko kuma sun watsu ne a duniya saboda yanayi na hijira ko rashin yancin.

Akidar tana farkarwa wajen sanin asali da tushe fiye da samun ilimi kan batun, da ya hada mutane karkashin wata tuta da aka yi guda.

Maganar Tarihi:

Pan-Africanism, wani yunkuri ne da ya fito a karshen karni na 19 zuwa farkon karni na 20, yana wakiltar wata kafa mai karfi da ta samo asali a cikin gwagwarmaya da muradi da kuma burin daidaikun mutanen Afirka a duk fadin duniya.

Domin fahimtar muhimmancin akidar, dole ne mu yi waiwaye mai zurfi cikin tarihi.

Tafiyar Pan-Africanism yana karfafa hada kai a tsakanin 'yan yankin. Hoto: AFP

Yunkurin ya samo asali ne bayan irin abubuwan da suka faru a zamanin mulkin mallaka da lokacin bautar bayi da kuma rashin adalci na nuna wariyar launin fata.

Akidar Pan-Africanism ya bullo ne a matsayin martani ga ire-iren kalubalan da al'ummar Afirka suka fuskanta a duniya.

Akidar ta samar da dandali ga wadanda abin ya shafa domin su hada kai tare da magance matsalolin da suka addabi al’ummarsu.

Kalmar ''Pan''-Africanism yana nufin hadawa ko fadadawa, da duniya baki daya.

Kamar tana nufin rungumar dukkan wani nau'in al'adu na Afirka iri daban-daban - ta hanyar toshe bambance-bambance na kabilanci da iyakoki na kasa da kuma raba kan al'umma.

Pan-Africanism na jan hankulan al'ummar Afirka da su fahimci kansu ba kawai ta hanyar kabila ko kasa ba amma a matsayin wani babban bangare na dangin Afirka masu alaka da juna.

Raba gado da Al'ummar Afirka da zama a Kasashen waje

Yana da mahimmanci a yi tuni da tarihin al'ummar Afirka da suka kaura zuwa kasashen waje da yankin Caribbean, inda aka tilastawa mutane da dama barin yan'uwansu na asali a Afirka kana aka sayar da su don yin bauta a kasashen waje.

Akidar Pan Africanism tana taimakawa 'yan Afirka da ke zama a kasashen waje su samu damar gano asalinsu da tushensu a Afirka tare da ba su damar kwato gadonsu.

Ta hanyar sanin ainihin jinin da ke gudana a jikinku na Afirka, daidaikun mutanen da ke kasashen waje za su iya karfafa Akidar Pan-Africanism, ta yadda za a fahimci cewa, su wasu bangare ne na babbar al'ummar nahiyar Afirka.

Hoton tsohon shugaban Ghana Kwame Nkrumah da tsohon shugaban kasar Masar Jamal Abdul Nasser

Ka yi tunanin duniyar da mutum daga tsibirin Seychelles ko kasar Burkina Faso ko Nijeriya ko Kenya ko Afirka ta Kudu ko Masar ko Ghana ko kuma yankin Caribbean, ko a ce mutum bakar fata daga Amurka ya gabatar da kansa a matsayin dan Afirka ba tare da an bincike sa yare ko kabila da yankin da ya fito ba.

A lokuta da dama irin wannan yanayi da ake ciki kan aza ayar tambaya masu tarin yawa wanda ke kara haifar da rarrabuwar kawuna.

Ta hanyar bin akidar Pan-Africa, mutane za su iya zurfafa tare fadada tunaninsu da kuma fahimtar kawunansu a matsayin wani bangare na dangin Afirka da ya kunshi al'adu iri daban-daban da tarihi da kuma gudummawar da ake bayar wa.

Kamar yadda mutum zai iya danganta kansa da wata kasa ko kabila, haka kuma zai iya danganta Afirka a matsayin asalinsa ko wurin da ya fito.

Tasirin Pan-Africanism ya ta'allaka karkashin yada manufar akidar tare da samar da hadin kai, la'akari da tarin yawan al'umma da suka warwatsu a fadin duniya.

A nahiyar Afirka kadai akwai sama da mutum biliyan daya, sannan akwai miliyoyin 'yan nahiyar da suka bazu a kasashen waje, da yankin Caribbean zuwu yankin Amurka da Turai.

Rungumar wannan asali zai kara hada kan mutane tare da ba su damar zama mafi yawan al'umma 'yan uwan juna a duniya - 'yan'uwa masu arzikin hadin kai da kwazo da kuma ci gaba.

Hadin kai na Tattalin Arziki

Babban jigon Pan-Africanism ya ta'allaka ga amincewa da bukatun samun hadin kai a fannin tattalin arziki, tare da inganta hanyoyin zuba jari da kasuwanci a cikin nahiyar ta Afirka da kuma saukaka ci gaba al'ummomin Afirka.

Ta hanyar amfani da karfin tattalin arziki nahiyar baki daya, masu akidar 'pan- Afircanism na kokari wajen kawo karshen dadadden tahirin sata da tabarbarewar albarkatu da suka janyo wa Afirka cikas a samun ci gabanta.

Ko da yake, hanyar samun wannan hadin kai ba na mutum daya ba ne kawai; akwai bukatar samun hadin kai daga kungiyoyi kamar kungiyar Tarayyar Afirka Au da sauran kungiyoyin Afirka.

Ilimi na zama abu muhimmi da ake bukata a wannan fage- don fadakar da mutane game da tasirin Pan-Africanism, ba wai a matsayin wani tunani ko ra'ayi ba amma a matsayin wani bangare na sanin asalin da tushensu.

Tamkar kira ne ga ’yan Afirka maza da mata su zama 'yan uwan juna.

Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo, daya daga cikin kasashe mafi arziki a fannin ma'adanai na da burin ceton masu hakar ma'adinan cobalt daga 'yan damfara. Hoto: AFP

A zahiri akidar Pan-Africanism ba ra'ayi ba ne da za a tattauna a cikin manyan dakunan taro ko kebabbun wuraren ba da ilimi; kira ne zuwa ga aiki, sannan yunkuri ne zuwa ga samun makoma mai kyau idan aka hada kai.

Tafiya zuwa ga hadin kan 'yan Afirka na bukatar tunani mai zurfi da tausayawa da kuma gudumawar kowa don sake fayyace asalinmu ba tare da takaitawa zuwa iyakoki da kabilu ba.

Akwai bukatar a koyar da duk wani 'dan Afirka ba tare da la'akari da kabila ko kasa da ya fito ba yadda zai na bayyana kansa a matsayin 'dan Afirka.

Akidar Pan-Africanism da kungiyar Tarayyar Afirka

Ya kamata Pan-Africanism ya zama ginshikin kungiyar Tarayyar Afirka, kungiyar da ta himmatu wajen samar da hadin kai da kuma hadin gwiwa a fadin nahiyar.

Ta hanyar sanya Pan-Africanism a tafiyarta, kungiyar AU za ta iya ba da fifiko ga muradun dukkan 'yan Afirka tare da kokarin samar da hadin kan Afirka wanda ya zarce iyakokin kasa da kabila da kuma tarihin mulkin mallaka da ta gada.

Yunkurin hadin kai na 'Pan-Africanism' yana jaddada muhimmancin rawar al'adu da asalin nahiyar. Hoto: AFP

Idan har aka rungumi akidar Pan-Africanism a matsayin wani yunkuri na ainihin asali, ba ra'ayin wani ba, to ba shakka an share hanya zuwa ga lokacin da mutane za su gabatar da kansu cikin alfahari a matsayinsu na 'yan Afirka, tare da tsayin daka kan irin al'adunsu da kuma gina martabansu a idon duniya.

Wannan ba mafarki ba ne; hakikanin gaskiya ce ta zahiri da ke jiran hadin kanmu -ta yadda ba za a samu wata baraka ba, kuma 'yan'uwa mafi girma a duniya su kasance tare. tsinsiya daya, madaurinta daya.

Marubucin, Nana Dwomoh-Doyen Benjamin, Babban Darakta ne a cibiyar samar da bayanai na Afirka.

Togaciya: Ba dole ba ne ra’ayin marubucin ya zo daidaida ra’ayi ko ka’idojin aikin jaridar TRT Afrika.

TRT Afrika