Akwai kalubale da dama ga harkokin sufuri na haya a Afirka. Hoto: Gift Dumedah

Daga Gift Dumedah

Ababen hawa na haya na da matukar muhimmanci da ke taimakawa wajen samun ayyukan yi, karfafa gudanar da ayyukan hidimta wa jama'a, kula da lafiya, ilimi da damarmakin zamantakewa, wadanda ke da matukar muhimmanci wajen ingancin rayuwa da bunkasar ta.

A matsayin jigo ga samar da damarmaki, ababen hawa na haya na da muhimmanci wajen samar da ci-gaba mai dorewa, jin dadin jama'a da habakar kowa da kowa.

Akwai kalubale da dama ga ababen hawa na haya a dukkan duniya, amma matsalolin sun fi yawa a kasashen Afirka da dama.

Wajabcin aiki da wasu ka'idoji da hukumomin kudi na duniya suka sanya wa kasashe kafin su ba su bashi a shekarun 1980 da 1990, ya janyo rushe kamfanonin sufuri da dama na gwamnati.

Haka kuma, yawaitar bukatar ababen hawa na haya sakamakon yawaitar jama'a, samar da birane, karuwar unguwanni marasa jama'a a biranen Afirka sun sanya jama'a sun saba amfani da ababen hawa na ta-ci-barkatai.

A yayin da wannan tsarin sufuri na gargajiya ya bayyana, ya kunshi kananan motocin bas, tasi, babura da A-Daidaita-Sahu, wadanda ake kira a Turance da paratransit.

Wadannan ababen hawa ne suka fi biyan bukatar jama'a, inda a Cape Twon kaso 58 na jama'a, a Nairobi kaso 87, a Accra kaso 86 ne ke amfani da irin wannan tsari na sufuri.

Kutse ga harkokin sufuri

A wasu biranen Afirka akwai tsarin yi wa manyan motocin bas hanyarsu su kadai, (BRT) kamar a Legas da ke Nijeriya, Darussalam da ke Tanzania, Tshwane a Afirka ta Kudu da ma wasun su.

Tsarin sufuri na gargajiya ya bayyana, ya kunshi kananan motocin bas, tasi, babura da adaidaita sahu. hoto: Gift Dumedah

Tsarin na BRT na amfani da hanya daya kawai ga motocin, yana bayar da dama a yi tafiya cikin sauri, kuma motocin na da girma, suna daukar mutane da yawa cikin yalwa da jin dadi.

Ana yi musu kallon wadatattu, masu daukar jama'a da yawa, kuma fata nagari ga dorewar harkokin sufurin zamani a Afirka.

Amma tsarin BRT na yanzu wani bangare ne na aikin sauran kananan ababen hawa na haya.

Ma'ana tsarin kananan ababen hawa ne ya fi amfanar jama'a a Afirka. Tsarin na da muhimmanci ga kasashen Afirka da dama, kamar yadda da wahala su yi ayyuka ba tare da wadannan motoci na haya ba.

Duk da rawar da suke takawa wajen kai komon jama'a, kananan ababen hawa na haya a Afirka ba su da inganci inda suke janyo rashin wadatattun damarmaki, cunkoson ababen hawa, hatsari a kan hanyoyi, rashin ingantaccen tsarin gudanar da ayyukan su, da rashin kyawun hanyoyi.

Babban sauyi

Tun tale-tale, akwai manyan kalubale da ke addabar harkokin ababen hawa a Afirka, wasun su na da alaka da rashin kyakkyawan shugabanci, rashin kudade, rashin kayan more rayuwa, rashin mayar da hankali wajen inganta harkar sufuri a tsakanin jama'a da ma karancin ababen hawar na haya.

Harkokin sufuri a Afirka ba sa samun zuba jari yadda ya kamata. Hoto: Gift Dumedah

Ana bukatar babban sauyi ga tsarin sufurin ababen hawa na haya. Tsarin ne yake bayar da damar kai komo mafi girma ga kasashe, amma kuma ba ya samun kulawar da ta kamata daga mahukunta, babu tsari, babu zuba jari da tabbatar da isassun kudade da ma gine-gine don amfanin ababen hawar da matafiya.

A duniya, ababen hawa na haya da suka hada da kananan motocin bas, tasi, babura da A-Daidaita-Sahu sun zama masu inganta rayuwar mutane, a saboda haka suna bukatar kulawa ta hanyar amfani da kudaden gwamnati.

Babbar illar wannan abu mara dadi shi ne kowa na illatuwa da tsarin sufurin ababen hawa na haya da ba shi da inganci.

Fasinjoji na shan wahala wajen amfanin da wadannan ababan hawa marasa inganci inda masu sana'o'i suke wahalar jure ababen hawar marasa inganci.

Sannan ana samun gurbata muhalli sosai, karuwar cunkoso da hatsarin ababen hawa, raguwar hanyoyin samun damarmaki da yanayin sufuri mai cutarwa.

Akwai tsarin sufuri na gargajiya a Afirka. Hoto AFP

Sai dai kuma, akwai damarmaki ga makomar ababan hawa na haya a Afirka.

Bukatar juriya

Har yanzu ana ci gaba da gina tsarin sufuri a Afirka. Ana fatan samar da tsarin da zai shiga kowanne bangare tare da inganta sufurin ababen hawa na haya musamman ma kananan motocin bas, tasi, babura da A-Daidaita-Sahu.

Akwai kuma yiwuwar shigar da tsarin sufurin ababen hawa na haya ga karfafa alakar hadin kan fasahar kere-kere, karfafa gwiwa ga zuba jari da ci-gaban sufuri, sannan da sake nazari kan manufofin sufurin ababen hawa na haya daga mahukunta.

Yana da muhimmanci cewa wadannan ayyuka za su tabbatu ne ta hanyar zuba jari da samar da kudade, kokarin rage zafin tattalin arziki, zamantakewa da muhalli.

Haka kuma tsarin sufurin ababan hawa na haya a Afirka da zai zo nan gaba na bukatar jure ibtilao'in da ka iya afkuwa, rikicin duniya, matsalolin kudade, sauyin yanayi da illolinsa.

A karshe, babban burin da ake da shi shi ne samar da tsarin sufuri ga jama'a da kowa zai amfana, mai inganci, mai dorewa da juriya a Afirka.

Marubiya Gift Dumedah Malamar Jami'a ce a Ghana, wadda bincikenta ya mayar da hankali kan sufuri da kai komo a Afirka.

Togaciya: Ba dole ba ne ra’ayin marubucin ya zo daidaida ra’ayi ko ka’idojin aikin jaridar TRT Afrika.

TRT Afrika