Daga Leyla Hamed
A farkon wannan watan, an tsara FIFA za ta yi masa tare da yanke hukuncin ko za a dakatar da Isra'ila daga harkokin wasanin kasa da kasa saboda laifukan yaki da keta hakkokin dan'adam wanda ya saɓa wa sharuda da dokokin kungiyar.
Amma gaskiyar lamari cikin nuna tsoro, sai ga shi FIFA ta dage zaman har sai bayan gasar wasannin tsalle-tsalle ta Olympic, suna baiwa kasar kariya daga tuhuma.
A watan Afrilu, Kungiyar Kwallon Kafa ta Falasdin ta yi kira ga FIFA da ta saka takunkumi ga Isra'ila tare da dakatar da ita daga shiga harkokin FIFA saboda keta harkokin dan adam da karya dokokin kasa da kasa.
Maimakon haka, kungiyar kula da kwallon kafar ta dauki matakin jinkirta daukar matakin a watan Yuli, duk da cewar kungiyar na da tarihin dakatar da Rasha cikin 'yan makonni da afka wa Ukraine.
A wata sanarwa, FIFA ta ce "Bayan bukatar tsawaita lokacin da kowanne bangare zai mika matsayinsa, kuma FIFA ta amince da hakan, to ana bukatar karin lokaci don kammala wannan aiki cikin nutsuwa."
A yanzu sai a karshen watan Agusta za a sake duba wannan batu.
Amma, mutanen da suke kusa da mahukuntan na cewa rahoton da kwararru kan shari'a na FIFA suka bayar ya shiga hannun hukumar mako guda kafin fitar da sanarwar.
Ko ma dai meye, babu mamakin daukar wannan mataki.
Tun da fari hukumar kwallon kafar falasdin (PFA) ta fito karara ta mika bukatar neman a dakatar da Isra'ila daga taron FIFA d aaka gudanar a watan Mayu a Mangkok, amma sai FIFA ta bayar da aikin bincike ga lauyoyinta.
Maimakon bayar da dama ga mambobinta 211 su jefa kuri'a kamar yadda aka saba, sai FIFA ta mika yanke hukuncin ga majalisarta.
Wannan majalisar ta kunshi mambobi 37 ne kawai kuma amintattun shugaban FIFA Gianni Infantino, shugaban kungiyar kwallon dan kasashen Italiya da Switzerland, kuma an san shi da zama mai goyon bayan Isra'ila.
Kalaman tsana
Yadda FIFA ta dage yanke hukuncin ya baiwa Isra'ila damar halartar gasar wasannin tsalle-tsalle ta Olympic ta 2024 a Paris.
Mummunan abinda ake da shi a nan shi ne dukkan 'yan wasan kwallon kafar Isra'ila, sojojin kasar ne. Aikin soja dole ne ga duk wanda ya kai shekara 18 a Isra'ila, kuma duk wadanda ba su je sojan ba, ba a ba su damar shiga kungiyar kwallon kafar ta kasa.
Da yawa daga cikin 'yan wasan da ke taka leda a kungiyar Isra'ila, sojoji ne da ke bakin aiki a rundunar sojin Isra'ila, kuma suna da hannu a hare-haren da suka saba wa dokokin kasa da kasa a Gaza.
Wasu magoya bayan kwallon kafa ba su da alhakin matakan da gwamnatocinsu suke dauka. Da yawa na tallata sojojin isra'ila tare da ingiza kisan kiyashin da ake yi a shafukansu na sada zumunta.
Misali, a watan Nuwamba, Shon Weissman, tsohon Sojan Saman Isra'ila kuma dan wasan kwallon kafa na kungiyar Salernitana da ke Italiya d akuma kungiyar kasa ta Isra'ila ya fitar da wani sako a shafinsa na X da ke cewa "Wanne dalili ne ya sanya har yanzu ba a jefa bam mai nauyin tan 200 a Gaza ba?", ya kuma amsa da cewa "Ku rusa, Ku Tsaurara, Ku mittsike. Ga daukar fansar Ubangiji."
Haka kuma abokan buga kwallon kafarsa, Tomer Yosefi daga Hapoel Haifa FC a Isra'ila ya ce "A wannan lokacin za mu shafe Gaza gaba daya."
Irin wanan kishiryar jini ba daga 'yan wasa maza kawai ke fitowa ba. Wasu 'yan kwallon kafa mata na Isra'ila ma sun dinga yada bidiyo da hotunansu suna cire kayan kwallo suna saka na sojin Isra'ila
Wadannan misalai na ingizawa da tsarkake sojoin Isra'ila da 'yan wasanta ke yi na tafiya ba tare da wani hukunci ba daga Hukumar Kwallon Kafar Isra'ila (IFA).
Wannan na faruwa ne duk da cewar IFA na aiki da dokokin ladabtarwa na FIFA, inda sashe na 53 ya haramta ingiza rikici ko kalaman nuna tsana.
Amma kuma an tirsasawa 'yan wasa daga Rasha da Belarus kan lallai sai sun yi aiki da ka'idar 'kin nuna bangaranci', shiga gasar ba tare da daga tuta ba, alama ko yin taken kasa.
Dadin dadawa, Sase na 4(1) na dokokin FIFA ya haramta "nuna wariya ga wata kasam wani mutum ko wata kungiya sabod alaunin fatarsu, yare, kasa ko asalin al'ummar da suka fito daga cikinta... hakan ya haramta kuma ana hukunta wanda ya yi ta hanyar dakatarwa."
IFA ta gaza aiki da wadannan dokoki, kamar yadda ake gani daga 'yan wasan kwallon kafar Isra'ila daga kungiyoyin Jeruselem, Beltar Jerusalem FC, kuma mai taka leda a gasar Zakarun Isra'ila.
Magoya bayan kungiyar na rera wakoki kan yadda suka zama "kungiya mafi nuna wariyar launin fata" a Isra'ila kuma suna yawan kiran Larabawan da ke buga ƙwallo a wasu kungiyoyin da 'yan ta'adda'.
Kungiyar kwallon kafar Isra'ila ta kuma hana Larabawa shiga kungiyar, sannan matakan ladabtarwa ne kawai ake dauka idan aka yi wani mummunan abu ga Balarabe dan wasa.
Amfani da wasanni don halarta mamaya
Tun kafin 7 ga Oktoba, FIFA na da kwararan dalilan da za su sanya ta kori Isra'ila.
Sashe na 72(1) na dokokin FIFA sun ce, "kungiyoyi mambobi da 'yan wasansu ba zansu buga wasanni a iyakokin waa mamba ba ba tare da yardar wannan mamba din ba."
FIFA ta san cewa IFA na karya dokokin FIFA tun 2013, ta yadda suka baiwa Isra'ila damar buga wasanni a yankunan da ta mamaya ba bisa ka'ida ba.
Akalla akwai kungiyoyi biyar a yankunan Falasdinawa da aka mamaya: Kyriat Arba, Givat Zeev, Ariel, Bikat Hayarden da Ma'aleh Adumim.
Infantino, shugaban kungiyar kwallon kafa ta duniya, ya yi biris da wannan batu, duk da cewa wannan batun na da muhimmanci ga siyasa da harkokin wasannin yankin.
FIFA na da alhakin tabbatar da ba adinga karya dokokinta na kare hakkokin dan adam ba. Ta hanyar daukar nauyin wasanni a kasar da aka kwata ta karfi da yaji daga wajen Falasdinawa d akuma karbar bakuncin wasanni a karkashin yanayin nuna wariya, FIFA na karya dokokinta da kanta.
Kisan kiyashi a Gaza
A Gaza, keta hakkokin dan adam da Isra'ila ke yi sun kai wani sabon mataki mummuna.Tun 7 ga Oktoba, Isra'ila ta kashe Falasdinawa sama da 41,000 da suka hada da yara kanana 16,000.
An jikkata sama da Falasdinawa 86,000 inda har yanzu wasu mutanen 10,000 suke karkashin buraguzan gine-ginen da hare-hare suka rusa.
Harkokin wasannin Falasdinawa ba su tsira daga zaluncin da Isra'ila ke ci gaba da yi ba.
A watanni taran da suka gabata, an rusa ko lalata filayen wasannin Gaza guda 41, sun zama ko sansanin 'yan gudun hijira, wajen daure mutane ko ramukan binne jama'a da yawa.
A watan Disamban 2023, an ga wani bidiyo d ake nuna sojojin Isra'ila na mayar da filin wasa na Yarmouk zuwa wajen duare mutane, inda suka yi wa maza da mata da yara kanana kusan tsirara tare da duare fuskokinsu, yayin da dakaru da tankokin yaki suka kewaye wajen.
Alkaluman PFA sun bayyana cewa an kashe 'yan wasansu 400 tun 7 ga Oktoba, ciki har da 'yan wasan kwallon kafa 243, 65 daga ciki yara ne kanana.
Wadanda aka kashe din sun hada da nazir al-nashnash, dalibin jami'a mai shekara 20 da ke buga wasa a kungiyar Bureji Services da Hani Al-Masdar, tsohon dan wasa kuma mai bayar da horo a kungiyar kwallon kafar Falasdinawa.
Kun tina Afirka ta Kudu?FIFA ta taba dakatar da gwamnatin farar fata 'yan tsiraru, kuma hakan ya taimaka wajen rusa tsarin. An kafa tarihi a wannan lokacin. Kamar dai yadda FIFA ta dauki mataki cikin sauri kan Rasha kwanaki hudu bayan afka wa Ukraine.
FIFA na karkashin matsin lamba sabod ayadda ba ta da niyyar daukar mataki da tuntuni aka makara daukar sa. ta yaya za su yi bayanin nuna bambanci sabod aan zo batun dakatar da Isra'ila?
Leyla Hamed 'yar kasar Spaniya ce kuma asalinta a 'yar Morocco ce kuma 'yar jaridar da ke dakko labaran wasannin kwallon kafa da dokokin wasanni wadda ke rayuwa a Ingila. A yanzu tana aiki a matsayin edita, marubuciya da sharhi kan Wasannin Tsalle-Tsalle, tana dakko rahotanni daga Gasar Premier.
Togaciya: Ba dole ba ne ra'ayin marubucin ya zama daidai da ra'ayi ko dolokin aikin jarida na TRT Afrika ba.