Daga Eraldo Souza dos Santos
A watan Maris na 1967, ɗalibin jami'ar Columbia Bob Feldman ya gano wasu takardu a ɗakin karatun jami'ar da suke cikakken bayani kan haɗin gwiwarsu da Cibiyar Nazarin Tsaro, wata ƙungiya mai alaƙa da Ma'aikatar Tsaron Amurka.
Ɗauke da isassun hujjoji, Feldman, tsohon ɗalibin Nazarin Dimokuraɗiyya, sai ya tattaro abokansa zuwa ƙaddamar da gangamin nuna adawa ga yaƙi. Tsawon shekara guda, ɗalibai suka yi ta neman lallai jami'ar ta yanke hulɗa da cibiyar, wadda ke goyon bayan yaƙin da Amurka ke yi a Vietnam.
A yayin da Jami'ar ta buƙaci toshe bakunan masu zanga-zangar adawa da yaƙin tare da murƙushe su a makarantar, cibiyar SDS da SAS sun gayyaci ɗaliban Barnard da Columbia kan su gudanar da sabuwar zanga-zanga.
A ginin da aka mamaye na Sorbonne ko a kan titunan Cape Twon, Prague, Rio de Janeiro da Tokyo, buƙatar ɗalibai ta bambanta, amma mafi yawansu na da manufa iri ɗaya.
Sun so su tunkari yadda ake nuna fifikon farar-fata da sabon tsarin mulkin mallaka, don kawo ƙarshen yaƙin Vietnam, su dakatar da aikin ƙera makaman nukiliya, da kuma kifar da gwamnatocin kama-karya da suka yaɗu a lokacin yaƙin cacar baki. Ɗaliban Columbia da Barnard wani ɓangare ne dukkan wannan gwagwarmaya a faɗin duniya.
Ƙalubalantar masu nuna fifikon farar-fata
Ƙasa da shekaru ashirin bayan hakan, a watan Afrilun 1985, Columbia ta dawo bakunan kafafen yaɗa labarai a lokacin da mambobin Gamayyar Kuɓutar da Afirka ta Kudu suka yi sarƙa da toshe ƙofofin babban ɗakin taro na Hamilton don gudanar da zanga-zangar adawa da zuba jarin jami'ar a Afirka ta Kudu da ke ƙarƙashin masu nuna fifikon farar-fata.
Bayan wasu 'yan watanni, sama da masu zanga-zanga 200 ne suka ɓoye musu. Ɗalibai bakwai da suka yi zaman dirshan a wajen suna azumi na tsawon kwanaki. Martanin da mahukuntan jami'ar suka mayar shi ne "Ku ci gaba da azumi." Zanga-Zanga a gine-ginen makarantun Amurka da dama sun wanzu.
"Ba a sabo da irin wannan rashin biyayyar," Marthin Luther King Jr ya taɓa yin muhawara a wani babin na daban. Ɗaliban Columbia da Barnard da ma can sun saba nuna tirjiya ga yaƙi."
Al'ada ce da suke cewa jami'o'insu na yin bikin tunawa da su da munar su shekaru da dama da suka gabata. A karo na biyu, ɗaliban Amurka na koma su zama masu gwagwarmayar siyasa.
Amma abin da ke faruwa a jami'ar Columbia wani ɓangare na tarihin kwanan nan.
Zamanin rigingimu
Tsawon shekaru an siyasantar da yadda ɗalibai matasa yau a Amurka suke ta yaɗuwa a jami'o'i suna kafa sansanoni.
Sun girma a lokacin da ake bayyana kasuwar samun aika na rugujewa, batun daidaito ko adalci ma babu shi da sunan nuna wariya ko jinsin mutum, kuma al'ummun da suka wuce ba su taɓuka komai ba wajen yaƙi da rikicin sauyin yanayi.
Wannan zamani ne da ya ma fi na waɗanda suka mamaye Columbia a 1968 da 1985, sun koyi karatu a azuzuwan makarantunsu kan cewa za su iya sukar jami'o'in, da ma irin rawar musamman da jami'a za ta iya takawa.
Sabon zamanin farfesoshi, mafi yawansu mambobin ƙungiyoyin da ba a sani ba a fagen jami'o'in Amurka, sun gayyaci waɗannan ɗalibai kan su kula da tunanin cewa jami'o'i manyan wakilai ne na mamayar sojojin Amurka.
Kuma suna da hakkin yin tunanin haka: Jami'o'i da ke da albarka sosai sun zama kamfanoni. d ayawan su na zuba jari wajen samar da makamai da ke janyo rikici a duniya.
Sun kuma bayar da gudunmowa sosai wajen samar da ilimi game da al'adu, yaruka, da al'adun siyasa na yankunan da Amurka ta nemi ta fada ikonta a cikin su.
Mene ne abin yi?
Tuni aka fara ganin illar zanga-zangar da masu goyon bayan Falasɗinu ke yi a makarantun Amurka.
Waɗannan mutane dai masu tsaurin ra'ayi da sai kwanan nan suna haƙura da rabu da al'ada a manyan makarantun Amurka tare da rungumar sabuwar al'adar jami'a da ke kan tubalin 'yancin faɗin albarkacin baki, a yanzu su ne suke ƙoƙarin kamawa da ɗaure waɗanda suke sukar Isra'ila.
A yunƙurin da suke yi na ɗaukar matakan faɗaɗa yawaitar ra'ayoyi, daidaito da shigar da kowanne ɓangare na jami'o'in Amurka, 'yan tawayen masu tsaurin ra'ayi sun so nuna cewar jami'o'i suna goyon munanan ra'ayoyi da aƙidu ne.
A yanzu da suke alaƙanta ra'ayin ɗalibai na adawa da masu rajin nuna fifikon Yahudawa da kyamar Yahudawa da ta'addanci, suna ta ƙoƙarin jan ra'ayin jama'a kan cewar wannan shi ne batun.
Kuma yadda gwamnatin Biden ta alakanta wannan mummunan zato ga daliban Columbia na iya rura wutar dabbaka ra'ayin.
Mai yiwuwa kawai muna shaida farawar sabuwar gwagwarmayar dliban duniya da hakan zai iya sauya fasalin al'ummun Amurka da rawar da Amurka ke taka wa a duniya.
A shafukan sadarwa na zamani, gwamnatin Isra'ila na amfani da irin wannan tsari don murkushe alibai. Masu tsaurin ra'ayi da 'yan mazan jiya na duniya za su san yadda za su yi da hakan a ayyukansu na yau da kullum.
Tun shekarun 1960, gwagwarmayar dalibai ta sauya da sake sauya fasalin duniya, a mafi yawancin lokuta ta hanyar da ba a tsammata. a yanzu muna shaida gwagwarmayar dalibai a duniya da yiwuwar sake fasalin al'ummar Amurka da rawar da Amurka ke takawa a duniya.
Marubucin, Eraldo Souza dos Santos, ƙwararre ne a tarihin gwagwarmayar al'ummu a duniya. Mai Shirin Zama Babban Jami'in gwamnati a Jami'ar Cornell kuma mai shirin zama Mataimakin Farfesa a fannin nazarin laifuka a Jami'ar California, Irvine.
Togaciya: Ba dole ra’ayin marubucin ya zama ya yi daidai ra’ayi ko ka’idojin aikin jarida na TRT Afrika.