Daga Emir Hadikadunic
Jamus ta amince da ninka kayan ayyukan soji zuwa Isra'ila har sau bakwai a watanni uku da suka gabata, inda ta ci gaba da kasnacewa kasar Turai da ta fi tallafa wa Isra'ila a fannin soji.
Amma a yayin da ake ci gaba da yaki, masu suka da dama na tambayar me ya sa har yanzu Berlin ke kallon Isra'ila a matsayin babbar ƙawa, har ma a lokacin da ta kashe dubban Falasdinawa.
Fahimtar amsar na bukatar sake duba tarihi mai rikitarwa, wanda ya samo tushe daga abinda ya biyo bayan kisan kiyashi ga Yahudawa a lokacin Yakin Duniya na II, wanda ke bayyana nauyin da ke kansu na tabbatar da tsaron Isra'ila.
Sai dai kuma, idan aka kalli maganar masanin falsafa na Faransa Voltaire game da Daular Rumawa Mai Tsarki, wadda ba ta da tsarkin, ba ta Rumawa ba ce, kuma ba daula ba ce, za a iya muhawara kan yadda Jamus ke tallafawa ayyukan sojin Isra'ila - a yayin da ake zargin ta da ikata kisan kiyashi a Gaza - hakan ba ladabi kuma bai dace da doka ba. Kuma hakan ba ya inganta tsaron kowa.
A shekara dayan da ta wuce, Jamus ta amince da kai makamai Isra'ila har na dala miliyan 363.5, ninki goma sama da wanda aka kai a 2022.
Wannan ya kai kashi 47 na jimillar kayan yaki da Isra'ila ta shigar kasar daga kasashen waje, inda Jamus kuma ta zama kasar Turai da ta fi kowacce kai kayan yaki Isra'ila, inda ta zama ta biyu a duniya bayan Amurka.
Karan tsaye ga dokoki
Munanan ayyukan da aka yi a lokacin Yakin Duniya na II ya bar babban tabo a kwakwalwar Jamus, wanda hakan ke sanya ta yin duk mai yiwuwa don tabbatar da tsaron Yahudawa.
Wannan wajabci na Jamus yana daga manufofinta na kasashen waje, wanda ya kai ga bayar da manyan tallafin diolomasiyya, kudi da ayyukan soji ga Isra'ila. Sai dai kuma, wannan taimako da ba shi da wasu sharudda, ya saba wa dokokin Jamus.
Yadda Jamus ke tallafawa ayyukan soji na Isra'ila ba kakkautawa na cin karo da yadda take cewar tana aiki da dokokin kasa da kasa, wanda aka bayyana har sau 23 a kundin Dabarun Tsaron Kasa, da kuma mayar da hankalinta ga tsarin 'yanci - wanda ya sanya kasar zama mai yi karan tsaye, kuma ba ta nan ba ta can.
Haka zalika, Dokar Kula da Makaman Yaki ta Jamus ta tanadi cewa kar a yi amfani da makaman da ake fita da su kasashen waje don kashe fararen hula.
Amma duk da haka tana ci gaba da goyon bayan Isra'ila, wadda sojojinta suka kashe yara da mata a Gaza a shekara dayan da ta wucesama da yake-yaken da aka yi a shekaru 20 da suka wuce.
Yadda karara ake biris da rayuwar Falasdinawa, babu mamaki cewa Jamus na fuskantar kalubalen dokoki a yanzu haka.
Cibiyar Kundin Tsarin Mulki da Kare Hakkokin Dan Adam ta Turai a baya-bayan nan ta sanar cewa ta shigar da daukaka a Kotun Gudanarwa ta Frankfurt a madadin jama'ar Gaza, tana neman a dakatar da fitar da karin makamai a nan gaba.
Wani mazaunin Gaza da ya rasa matarsa da 'yarsa sakamakon hare-hare t sama da Isra'ila ke kaiwa, na cewa ci gaba da kai makamai na jefa rayuwarsa da ta sauran fararen hula, yana mai kira ga Jamus da ta dakatar da aika makaman.
Jamus ta kuma fuskanci tuhuma a Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Kasa da Kasa (ICJ) saboda zargin ta da "bayar da damar aikata kisan kiyashi" kan Falasdinawan Gaza.
Dadin dadawa, Berlin na fuskantar matsin lamba saboda karar da ke gaban ICJ na zargin isra'ila da aikata kisan kiyashi, da kuma zargin da ake yi wa Firaminista Benjamin Netanyahu da tsohon Ministan Tsaro Yoav Gallant na "aikata laifukan yaki da laifukan cin zarafin bil'adama".
Irin wadannan kalubale na dokoki da shari'a sun sanya sauran kasashen Turai, ciki har da Belgium, Italiya, Spaniya, da Netherlands, su dakata ko jingine fitar da makamai zuwa kasashen waje.
A watan Satumba, kotun Netherlands ta dakatar da dukkan fitar da kayan da ake samar da jirgin yakin F35 saboda damuwar ana amfani da jiragen wajen kai wa fararen hula hare-hare a Gaza.
Sabanin haka ga wadannan kasashe, Berlin ta yanke hukuncin yin biris da kalubalen dokoki tare da dawo da fitar da makamai sosai zuwa Isra'ila.
Domin dora alhaki babba kan matsyin halayyar Jamus, wannan kari na fitar da makamai ya zo daidai da lokacinda rikicin Isra'ila ya yi tsamari a Gaza da Lebanon a watannin Agusta da Satumban bana.
Zaman lafiya da karfi da ke cin karo da manufofinsu
Ministan Tsaro na Jamus Boris Pistorius a farkon shekarar nan ya bayyana cewa "Dole ne ba tare da bata lokaci ba mu yi duk mai yiwuwa don dawo da zaman lafiya a yankin."
Yadda ya nuna ya damu da a samar da zaman lafiya, yana da wahala a ya tafi tare da goyon bayan da Jamus ke bai wa Isra'ila.
Cibiyar Bincike Kan Tsaro ta Stockhom ta ce kudaden da isra'ila ke kashewa ayyukan soji ninki biyu na kasashe hudu makotanta da ke adawa da ita ne. Kazlaika, wannan majiya ta rawaito cewa Isra'ila na kashe wa sojojinta kudi ninki ukun wanda abokiyar adawarta Iran ke kashe wa nata sojojin.
Wannan rashin daidaito wajen kashe wa dakarun soji kudi na kawo tambayoyi masu muhimmanci. Idan ana sa ran daidaton karfi tsakanin abokan gaba zai kawo aman lafiya, a kalla ko da a rubuce ne, to me tallafin Jamus ke nufi wanda ke kara girman rashin daidaiton?
Hakan na iya nufin sakamako guda daya kawai: Jamus, kamar Amurka, na son Isra'ila ta dinga zaluntar makotanta.
Abinda ake nuna wa a matakin samar da tsaro ga isra'ila da dawo da zaman lafiya na iya bayyana bukatar mayar da Isra'ila ta zama jagora a yankin. A yayinda shugabannin Jamus ba su bayyana niyyarsa karara ba, amma ana iya ganin su a bayyane.
Muryoyi masu cin karo da juna
Amma a gida, doyon baya ga fitar da kayan yaki da Jamus ke yi na raguwa, a yayin da damuwa ke karuwa kan rikicin yankin baki daya.
Wani binciken jin ra'ayin jama'a a Jamus ta gano cewa kashi 60 na wadanda suka bayar da amsa sun nuna rashin amincewa ga bai wa Isra'ila makamai.
Kashi 31 ne kawai suka nuna suna goyon bayan matakin aika makamai ga Isra'ila, inda kashi tara suke tsaka-tsaki.
An gudanar da wannan kuri'a ta jin ra'ayin jama'a bayan wani rahoto ya bayyana cewa gwamnatin Firaminista Olaf Scholz ta yanke shawarar kara yawan makaman da kasar ke aika wa Isra'ila.
Duk da irin yadda ta zama mai rikici da takalar yaki, gwamnatin Jamus ta nuna amincewa da tabbacin da iIsra'ila ta ba ta na wadannan makamai ba za a yi amfani da su ba wajen kashe fararen hula.
Kakakin Ma'aikatar Harkokin Waje Sebastian Fischer ya jaddada cewa wannan mataki da cewa "Ba mu ga alamun cewa Isra'ila na aikata kisan kiyashi ba a Gaza."
Wasu jam'iyyun siyasa da masu nazari sun ce wannan taimakon soji ga Isra'ila da Jamus ke bayarwa zai karu sosai.
Niema Movassat, wani dan siyasa daga jam'iyyar masu saukin ra'ayi, ya soki Firaminista Scholz inda ya ce "Yunwa na addabar mutane a Gaza, Gaza ya zama wajen da ba zai zaunu ba, Isra'ila na kai wa Lebanon hari, UNIFIL na fuskantar hari daga sojojin Isra'ila.
Yayin da a Jamus, akwai tattaunawa sosai game da bayar da kyautar kayan yaki saboda wadannan keta dokoki na kasa da kasa da ake yi. Na rasa ma me zan ce."
Mai nazari kan harkokin siyasa Torsten Menge ya soki Mataimakin Firaminista Robert Habeck da Ministar Harkokin Waje Annalena Baerbock, yana mai cewa "Idan har Baerbock da Habeck za su bukaci tabbaci a rubuce daga Isra'ila cewa ba za ta yi amfani da makaman da Jamus ke ba ta ba wajen aikata kisan kiyashi, to lalle sun san cewa akwai yiwuwar Isra'ila na aikata kisan kiyashin."
Wasu masu suka a ciki da wajen kasar na cewa goyon bayan Jamus ga gwamnatin Netanyahu na zubar da girman Jamus din, kuma na kara ware Berlin a fagen kasa da kasa.
Gadar da matsaloli ga kasa
A wajen Firaminista Scholz, fitar da makamai zuwa Isra'ila "Manufar Kasa ce ta Jamus". (Staatsräson).
Wannan matsaya ba shi da gwamnatinsa kawai take illata wa ba game da rikicin bil'adama da ake yi a Gaza, hakan na iya addabar Jamus tsawon zamaninnika.
Jamus na fuskantar hatsarin za a dinga tuna wa da ita matsayin mai aika makamai ga kasar da sojojinta suka kai hare-haren bam din nukiliya shifa, inda ta kashe yara kanana 17,000 a shekara guda kawai - wanda wannan ya sanya kasar barin nauyin da ke kanta na hana afkuwar bala'i a nan gaba bayan kisan kiyashi ga Yahudawa.
Isra'ila ta kashe a kalla falasdinawa 44,000, ta raba sama da miliyan biyu da matsugunansu, ta rusa sama da rabin gidajen Gaza, ta rushe kashi 87 na gine-ginen makarantu, ta yi ruwan bama-bamai kan jami'o'in Gaza 12, tare da kawar da tsarin kula da lafiya na yankin.
Duk da taimakon Berlin aka yi haka. Shin Jamus za ta iya zubar da girmanta sama da haka?
Emir Hadžikadunić a yanzu mataimakin farfesa ne a Sashen Kimiyya da Fasa na Jami'ar Sarajevo, Bosnia da Herzegovina. Kuma malamin wucin gadi ne a jami'o'i daban-daban a Bosnia da Herzegovina, Turkiyya da Malaysia. Dr. Hadžikadunić ya yi aiki da a matsayin jakadan Bosnia a Iran da Malaysia, kuma ya buga litattafai biyu, tare da makaloli da yawa ga kafafan yada labarai da mujallu.
Togaciya: Ra'ayoyin da aka bayyana a nan na marubucin ne, kuma ba sa wakiltar ra'ayi, komahangar editocin TRT Afrika.