Cool Fawa dake da mabiya da yawa a Tsakiyar Afirka na samun mabiya da dama a koyaushe da suke bibiya da rera wakokinta. Tana sanya tufafi masu jan hankali dake hade sama da kasa baki daya, kuma tana yin kyau sosai da kwalliyarta.
Mawakiyar gambarar da wakar zamani ta kaddamar da bakandamiyarta mai taken “Valide” (“Ingantacce”), kuma wakar ta ja mabiya da dama.
Wajen chashiyarta shi ne Bangui, babban birnin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya kuma a muhawarance dake da wahala ga mata dake neman shuhura.
A kasuwancin wake-wake da kade-kade, ana tafiya manyan birane don nuna basira da fasaha a kasashe masu arziki, kuma mashahurai za su yi amfani da yanar gizo wajen yada wakokinsu.
Idan za a dora a ma’auni, Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ba za ta shiga sahu ba.
Sama da shekaru 9 aka dauka ana tafka yakin basasar da ya kacalcala kasar.
Mutane kasa na daga cikin mafiya fuskantar talauci a ban kasa. Kaso 10 na jama’ar kasar su miliyan 5 ne suke samun yanar gizo.
Gambarar kawo sauyi
Wadannan matsaloli da kalubale ba su dakatar da Cool fawa ba.
Mawakiya da ta fara waka tun 2012 kuma take da shekaru 27 a yau, tana da mabiya sama da dubu 4,500 a Instagram, sannan a Youtube tana da ra’ayin mutane sama da dubu 50,000 a lokacin da ta saki wakarta maisuna “On va se marier” ma’ana (“Za mu yi aure”)
Irin wadannan mashahuran mutane ba su girmama ba, idan aka kwatanta da irin yadda ake bibiyar mawaka kamar su Adele, Beyonce ko Taylor Swift, amma idan ana maganar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ne, to lallai ta yi shuhura da kusan kowa ya san ta.
“Ina kaunar wakoki, suna sa min fatan wata rana zan yi nasara,” yarinya mai shekaru 16 ta fadi haka a wata mashaya dake Bangui.
Wani mutum ya yi ihu da cewa, “Cool Fawa, tana amon sauti”.
Cool Fawa da asalin sunanta Princia Plisson, tana waka a yaren Faransa da ta yi musu mulkin mallaka da kuma yarukan kasa na Sango da Turanci.
A lokacin da take hasashen makomar yin waka a shekarar 2010, a lokacin babu mawaka mata ‘yan asalin Jamhuriya Afirka ta Tsakiya.
Cool Fawa ta ce “Ina kaunar Diamis”, tana nufin mawakiyar gambara ’yar kasar Faransa, Melanie georgiades, wadda ta yi suna bayan fitar da jerin wakoki mai taken “Brut de Femme”, wanda ya kalubalanci duniyar maza.
Bayan daura aniyar bin sahu, matashiyar mawakiyar ta zama mace daya tilo a rukunin mawakan gambara maza masu rajin kawo sauyi, inda suka yi wakar tare da MC Functoinnaire,wanda wakokinsa sukeadawa da talauci da rashin adalci.
Ta ce “Da farko ba su dauke ni da muhimmanci ba amma a karshe kuma sun karbe ni.”
Amma ta kuma ce “Ana nuna kin wakokina, akwai iyayen da ma ba sa son ‘ya’yansu su kusance ni ko yin mu’amala da ni,”
Fita nema koyaushe
A cikin ‘yan shekaru, sai aiyukanta suka dusashe saboda yakin basasar kasar da ya barke bayan kifar da gwamnatin Francoir Bozize,
“Ba ma iya fita waje, muna tsoron kar a harbe mu ko a yi garkuwa da mu,” inji ta.
Bayan rikicin ya lafa, Cool Fawa ta dawo da zafinta, ta mayar da hankali kan wakokin alakar mata da maza, inda ta fara da wakar “Zouk love”, wani amo sauti na waka da ya faro daga Haiti ya yadu zuwa Caribbean.
“Wannan ne abun da yake sayuwa,” ta fadatare da yin nadama.
“A wajen mutane da dama a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, gambara wakar masu asara ce.”
Idan kana son ka rayuwa, kenan dole ka fita nema, domin neman kudi ba a gajiya da shi.”
Ta samu tallafi daga wasu makusanta, duk da tafi daga iyalai masu ‘yar wadata da yakana, kuma ta samu goyon baya kadan daga ma’aikatar raya al’adu.
Cool Fawa na da karamin kasuwancin da take gudanarwa da ‘yar uwarta.
“Muna sayen gashin doki, takalma, jakunkuna…. Daga waje mu sayar da su a nan. Wannan na ba mu damar na biya kudaden wakar da nake rerawa a dakunan rera waka a makociyarmu Kamaru.
Burinta shi ne ta fitar da sabon jerin wakokinta
Cool Fawa na samun na kashewa daga bukukuwan wakoki da ake shiryawa, amma kuma ba ta fara samun kudade daga wakokin da take bugawa ba akan Youtube musamman na bidiyo, saboda yadda jama’ar kasar ba sa samun yanar gizo yadda ya kamata.
Mahaifiyarta, Cecile Yohoram wadda malamar Turanci ce ta fadi cewa “Mutanen dake kewaye da ni a koyaushe na bayar da ra’ayi mara kyau game da abun da ‘yata ke yi,”.
“Amma da zarar na ji haka, sai na dinga alfahari”.