Gwamnatin Zimbabwe ta ce sabon kudin da ake kira ZiG zai taimaka wajen magance hauhawar farashin kayayyaki. Hoto: shafin X na ma'aikatar yada labaran Zimbabwe

Babban bankin ƙasar Zimbabwe ya ƙaddamar da sabbin “tsararrun takardun kuɗi” ranar Juma’a.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ƙasar ke ƙoƙarin shawo kan matsalar hauhawar farashin kayayyaki da kuma daidaita tattalin arzikinta da ya daɗe yana fama da tarin ƙalubale.

"Daga yau…Bankuna za su soma canza ma'aunin dalar Zimbabwe da ake hada-hada da shi zuwa sabon kuɗin, wanda za a kira shi 'Zimbabwe Gold' (ZiG), '' kamar yadda Gwamnan babban bankin ƙasar John Mushayavanhu ya bayyana a yayin da yake gabatar da sanarwar manufofin sabon kuɗin.

Ana sa ran matakin zai samar da ''sauƙi da kuma daidaito a harkokin kuɗin ƙasar," in ji shi.

TRT Afrika