Kamfanin fito na ƙasar Denmark, A.P. Moller-Maersk, ya amince ya zuba jarin $600m a tashoshin jiragen ruwa na Nijeriya, kamar yadda fadar shugaban ƙasar ta bayyana ranar Lahadi.
A.P. Moller-Maersk ya ayyana aniyar zuba jarin ne a ganawar da Shugaba Bola Tinubu ya yi da shugabansa Robert Maersk Uggla a gefen taron kasuwanci na World Economic Forum da aka gudanar a birnin Riyadh na Saudiyya.
"Mun yi amanna da Nijeriya, kuma za mu zuba jarin $600m a tashoshin jiragen ruwan ƙasar yadda manyan jirage za su samu damar zuwa," in ji Mr Uggla.
Shugaba Tinubu ya ce jarin da kamfanin zai zuba a tashoshin jiragen ruwan ƙasar zai ƙarfafa jarin dala bilian ɗaya da tuni aka sanya wajen inganta tashoshin jiragen ruwa a gabashi da yammacin Nijeriya.
Gwamnatin Nijeriya ta yi alƙawarin inganta tashoshin jiragen ruwan ƙasar, ciki har da waɗanda suke birnin Legas, cibiyar kasuwancin ƙasar, domin sauƙaƙa harkokin kasuwanci.
"Muna buƙatar ƙarfafa gwiwar 'yan kasuwa da dama domin faɗaɗa hanyoyin samun kuɗaɗen shiga da rage kwashe kayayyaki daga manyan jirage zuwa ƙanana," in ji Shugaba Tinubu.