Kasuwancin fitar da kafet na Turkiyya ya kai dalar Amurka biliyan 2.8 a shekarar 2024, adadin da ya kai murabba'in mita miliyan 589.2 na kafet da aka sayar, bisa ga bayanan da kungiyar masu fitar da kayayyaki daga yankin Kudu maso Gabashin Anadolu ta tattara.
Alkalumman da masana'antun kafet Turkiyya ke fitarwa sun nuna samun ƙaruwa da kashi 4.2 a shekarar 2024 daga shekarar 2023.
Kafet ɗin da ake yi da inji shi ne wanda aka fi fitarwa daga Turkiyya zuwa ƙetare da ya kai ake samun dala biliyan 2.2 na kudaden shiga, yayin da wanda ake yi da hannu ke biye da su, waɗanda a jumlace suka samar da dala miliyan 108.9 da dala miliyan 530.
Amurka ce ƙasar da aka fi kai kafet din Turkiyya, inda aka shigar da na dala miliyan 784. Saudiyya ce ƙasa ta biyu da aka fi kai kafet din Turkiyya inda aka kai na dala miliyan 287.2, sai Iraƙi na dala miliyan 265.3 da kuma Birtaniya na dala miliyan 187.5.
Sannan kuma kafet din Turkiyya da aka fitar zuwa Iraƙi a 2024 ya ƙaru da kashi 35,6 cikin 100 da aka saba fitarwa a shekara.
Yawan kafet din Turkiyya da aka fitar daga gundumar Gazianteo ya kai kusa dala biliyan biyu a 2024, yayin da na Istanbul da aka fitar ya kai dala miliyan 673.5, sai kuma na birnin Usak da ke arewa maso yammacin kasar da aka fitar da na dala miliyan 76.7.
Zeynal Abidin Kaplan, shugaban ƙungiyar ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na Anadolu cewa sun shirya tawagar kasuwanci ta ƙasashen waje tare da Amurka da Indiya da Australiya da Malaysia da Mauritania da Senegal da kuma Birtaniya kuma sun ji dadin irin bayanan da suka samu daga wajensu na amincewa da kayayyakin.
Sannan za a ƙara irin wannan taron jin bahasin da wasu ƙasashen da ma shirya tarukan ƙasa da ƙasa.