Tinubu ya bukaci a yi wa tsarin harajin duniya garambawul. / Hoto: AFP 

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya yi kira kan a yi wa tsarin harajin duniya garambawul, yana mai bayyana cewa yin gyara a rashin daidaito na tsarin harajin duniya ya zama wajibi.

Shugaban na Nijeriya ya jaddada sadaukarwa da kuma jajircewar kasarsa wajen samar da hadin kai don tunkarar kalubalen duniya.

Tinubu ya bayyana matsayin Nijeriya kan wannan batu a jawabinsa a taron Koli kashi na uku na kungiyar 77 da China wanda aka soma a ranar Kampala na kasar Uganda.

Ministan kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arzikin Nijeriya, Sanata Abubakar Atiku Bagudu ne ya wakilci shugaban a taron wanda aka yi wa take da "Ba za'a bar kowa a baya ba".

Tinubu ya yi kari da cewa batun haraji a duniya yana da matukar muhimmanci saboda yana shafar kasashe masu tasowa.

"A halin da ake ciki tsarin harajin duniya ya fi karkata ga bukatun kasashe masu arziki, sau tari da dama hakan na barin kasashe masu tasowa cikin mawuyacin hali, musamman wajen biyan harajin tattalin arziki na zamani.'' in ji shugaban na Nijeriya.

Yana mai ƙari da cewa ''rashin samar da daidaito a tsarin ya haifar da asarar kudaden shiga masu yawa, lamarin dake janyo cikas a kokarinmu na samun ci gaba mai dorewa da dogaro kan tattalin arziki. '' in ji shi.

Kan wannan batu, Nijeriya tare da sauran kasashe mambobin kungiyar Afirka, sun jagoranci wani gagarumin shiri mai cike da tarihi ga Majalisar Dinkin Duniya inda suka yi kira kan a samar da tsarin Harajin.

Kudurin a cewar shugaba Tinubu, wani muhimmin mataki ne wajen tabbatar da daidaito da kuma tsarin haraji na duniya baki daya.

Taron dai ya samu halartar shugabannin kasashe da gwamnotoci da dama da kuma shugabannin kungiyoyi na kasashen duniya da suka da hada da Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya MDD Antonio Guterres

A yayin da yake mika godiyar Nijeriya ga sauran kasashen da suka ba da goyon bayansu ga shirin yi wa tsarin harajin duniya garambawul, Shugaba Tinubu ya ce hadin kan da aka samu na nuna "jajircewarmu a ayyukan da muke da su na gyara kura-kuran da ake tafkawa a tsarin harajin da ake ciki da kuma samar da tsarin tattalin arziki mai adalci."

Kazalika, Shugaban ya jaddada kudurin Nijeriya na hadin gwiwa a fannin tattalin arzikin yankin Kudu-maso-Kudu.

Sannan ya yi tsokaci game da muhimmiyar rawar da kwamitin Action on Raw Materials (ACRM) na kungiyar G-7 da aka kafa a shekarar 1987 ke takawa don inganta hadin gwiwa a fannin bunkasa da sarrafa albarkatun kasa.

TRT Afrika