Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya rubuta wa Majalisar Dokokin neman ta amince a karɓo bashin naira tiriliyan 1.767 a matsayin shirin dokar kasafin kudi na 2024 na sabon rancen da za a ciyo daga waje.
Idan har majalisar ta amince, to za a yi amfani da bashin wajen cike giɓin kasafin kudin kasar na 2023 na naira tiriliyan 9.7.
Shugaban Majalisar Wakilai ne ya karanta buƙatar Shugaban Ƙasar a yayin zaman majalisar a ranar Talata.
Shugaban Ƙasar ya kuma miƙa wa majalisar ƙudurorin samar da Shirin Bayar da Tallafi na Ƙasa da kuma na MTEF/ FSP 2025- 2027, don aiwatar da shirye-shiryen gwamnatin tarayya na tallafa wa mutane.
Wannnan na zuwa ne a yayin da Babban Bankin Nijeriya CBN a kwanan nan ya ce Gwamnatin Tarayya ta kashe dala biliyan 3.58 don biyan bashin ƙasashen waje da ake bin ƙasar a watanni taran farko na shekarar 2024.