Asusun Ayyukan Cigaba na Saudiyya zai sanya hannu kan wasu yarjeniyoyi na riyal biliyan biyu, kwatankwacin dala miliyan 533 da ƙasashen Afirka.
Ministan Kuɗi na ƙasar Mohammed Al-Jadaan ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis, yayin wani Taron Tattalin Arziki na Saudiyya da Ƙasashen Afirka da ake gudanarwa a birnin Riyadh.
“Muna aiki da abokan hulɗarmu don tallafa wa Ghana da sauran ƙasashe kan batun basussukansu,” Jaddan ya ƙara da cewa.
Tun da fari a wajen taron, Ministan Zuba Jari na Saudiyya Khalid Al-Falih ya ce arzikin fiye da dala biliyan 700 da ke asusun na Saudiyya, zai yi tasiri matuƙa wajen “kawo sauyi na ban mamaki” a fannin zuba jari a Afirka.
Ministan Makamashi Yarima Abdulaziz bin Salman, shi ma a wajen taron ya sanya hannu kan wasu yarjejeniyoyi na farko da ƙasashen Afirka ciki har da Nijeriya da Senegal da Chadi da kuma Habasha don haɗin kai a abubuwan da suka shafi makamashi.