“Tuni muka fitar da wani tsari da za mu iya samar da yawan abin da suke so,” a cewar Ministan Harkokin Noman na Nijeriya. Hoto: Temitope Ajayi

Ministan Harkokin Noma na Nijeriya Mohammad Abubakar ya ce Saudiyya ta nuna sha’awar fara shigar da ton 200,000 na naman shanu da ton miliyan ɗaya na waken suya cikin ƙasarta duk shekara daga Nijeriya.

Minista Mohammed ya shaida wa manema labarai a ranar Alhamis a Abuja cewa Saudiyya ta nuna sha’awar hakan ne bayan da Ministanta na Harkokin Noma ya ziyarci Nijeriya tare da yin wasu taruka da ‘yan kasuwa a fannonin noma.

“Nuna sha’awar tasu kan wannan batu ke da wuya sai muka fitar da wani tsari da za mu iya samar da yawan abin da suke so da kuma biya musu buƙatarsu,” a cewar Ministan Harkokin Noman na Nijeriya.

Ya ƙara da cewa dama Nijeriya na neman abokan hulɗa na kasuwanci don samun kuɗaɗen ƙasashen waje bayan da ta sha fama da ƙarancin dalar Amurka, lamarin da ya yi mummunar illa kan tattalin arzikinta da kuma rage darajar kudin ƙasar na Naira sosai.

Nijeriya ta daɗe tana son raba ƙafa kan harkokin fitar da kayayyaki zuwa ƙasashen waje, maimakon fitar da ɗanyen man fetur kawai, wanda a yanzu fitar da shi shi kaɗai ba ya iya riƙe tattalin arzikinta sosai.

Reuters