An kammala yarjejeniyar biyan dala miliyan 783 na sayen kamfanin man fetur na Agip a Nijeriya da Oando ya yi./Hoto: Shafin X na Oando Plc

Kamfanin mai na Oando ya sanar da kammala biyan dala miliyan 783 don sayen wani reshen kamfanin Agip (NAOC) a Nijeriya.

Oando ya bayyana haka ne ranar Alhamis a wata sanarwa da babban jami’in kula da harkokin kamfanin kana sakataren kamfanin, Ayotola Jagun ya fitar.

Yarjejeniyar kammala cinikin dai ta bai wa, Oando wanda ke cikin jerin 'yan kasuwar da hada-hadar kuɗi ta Johannesburg Stock Exchange a Nijeriya, damar mallakar kashi 100 bisa 100 na hannayen jarin Agip daga kamfanin makamashi na Italiya, Eni.

Wannan muhimmin mataki ne na ''ci gaba'' ga babban kamfanin makamashi a Nijeriya Oando ta hanyar faɗaɗa ayyukansa tare da ƙarfafa matsayinsa a fannin mai da iskar gas a Nijeriya.

Oando ya bayyana cewa shekaru 68 bayan gano mai a Oloibiri, a yanzu ya shirya yin jagoranci tare da sarrafa kadarorin mai da iskar gas wanda a baya kamfanonin mai na duniya (IOCs) suka mamaye a Nijeriya.

Bisa ga sanarwar Oando, sayen kamfanin Agip ya bai wa kamfaninsa damar ƙara yawan hannun jarinsa daga kashi 20 har zuwa 40 a yarjejeniyar rijiyoyin mai a Nijeriya.

Kazalika, mallakar kamfanin ya ƙara wa Oando yawan hannayen jari a cikin duka kadarorin haɗin gwiwa na NEPL/NAOC/OOL waɗanda suka haɗa da rijiyoyin mai da iskar gas arba'in da aka gano, inda a halin yanzu 24 da aka ciki suke kan samar mai.

''Sanarwar yau ta cika yarjejeniyar shekara goma na ayyukan wahala da juriya da kuma imani mara misaltuwa kan cim ma burinmu na shekarar 2014 a yarjejeniya da muka sanya hannu kan kasuwancin haɗin gwiwa ta hanyar sayen rashen hannun jarin Conoco-Philips Nigerian Portfolio," kamar yadda shugaban rukunin kamfanin Oando Plc , Wale Tinubu ya bayyana.

"Nasara ce ga Oando, da duk wani mai ruwa da tsaki a harkar makamashi a Nijeriya, yayin da muke riƙe da makomarmu a hannunmu, kana muke taka muhimmiyar rawa a wannan fanni don ci gaban al'umma,'' in ji shugaban.

Wale Tinubu ya ƙara da cewa " da wannan matsayi da muka samu na aiki, za mu mayar da hankali kai tsaye wajen inganta damarmaki tare da haɓaka hanyoyi da kuma samar da dabaru da ba da gudunmawa a kadarorin da muke da ake da su.''

Kasuwancin zai samar da kuɗi nan take kuma ana sa ran zai ba da gudunmawa sosai ga shigar tsabar kuɗaɗe kamfanin.

TRT Afrika