Nijeriya za ta hada kai da Turkiyya wajen horar da masu sana'ar hannu mutum miliyan 20 a tsawo shekaru hudu/ Hoto:TRTAfrika

Daga Shamsiyya Ibrahim Hamza

A ci gaba da ƙoƙarin inganta dangantaka da ke tsakanin ƙasashen biyu, Nijeriya ta haɗa kai da Turkiyya domin inganta hanyoyin horar da masu sana’ar hannu a kasar wadda ke yankin Yammacin Afirka.

Gwamnatin Nijeriya karkashin Asusun Horar da Masana'antu Na Ƙasar (ITF) ta ƙuɗuri aniyyar horar da masu sana'ar hannu har mutum miliyan biyar a duk shekara na tsawon shekaru hudu domin su samu damar gogayya da ƙasashen duniya.

A wata ziyara da babban Daraktan ITF Dr Oluwatoyin Afiz Ogun da tawagarsa suka kawo Turkiyya sun gana da wasu manyan jami’ai a fannoni daban-daban domin kawo sauyi a hanyoyin koyarwa tare da bunƙasa fasahar masana’antu a Nijeriya a shirin na ITF da aka yi masa take da ''Skill-Up Artisans, ko SUPA Scheme.

Shirin dai ya kuduri aniyar horar da masu sana'ar hannu mutum miliyan 20 a tsawon shekaru hudu, tare da samar da takardar shaida da zai taimaka wajen samun aiki da kuma goggaya da kasashen duniya, kamar yadda babban Daraktan ITF ya jadadda a ziyarar da suka kawo Turkiyya.

A wata tattaunawa ta musamman da TRT Afrika Hausa ta yi da Dr. Ogun ya jaddada cewa, tawagarsa ta gana da manyan jami’ai a gwamnatin Turkiya da shugabannin masana'antu da kamfanoni da kuma cibiyoyin ba da horar da kwararru a fannin fasahohi, inda ya ce sun tattauna kan hanyoyin haɗin gwiwar da za ta taimaka wajen bunkasa ilimin sanin makamar aiki.

A nasu bangaren kuma, kwararru a Turkiyya za su ba da gudunmawar horar da kwararrun da za su koyar da masu sana’ar hannu a Nijeriya a bangarori daban-daban, in ji Dakta Afiz.

Nijeriya da Turkiyya sun shirya wani kawance mai cike da tarihi inda za su yi muyasar ilimi domin kawo sauyi a hanyoyin koyarwa

Ya yi karin haske kan tsarin samun gurbi a cikin wanna shiri da aka tsara, ''kusan masu sana’ar hannu 100,000 za su yi rajista a kowane mataki har sai mun cim ma adadin mutum miliyan biyar da muka yi ƙuɗuri a shekara, wanda shi ne babban burinmu na cika umarnin Shugaban Ƙasa Bola Tinubu,” in ji shi.

Wannan ƙawance zai taimaka wajen haɓaka hanyoyin koyarwa da ITF ke amfani da su ta hanyar kara martabar cibiyoyin ba da horo da tare da ba da shaida mai daraja wanda za a iya mafani da ita a ko ina a fadin a duniya wajen samun aiki.

Ziyarar da kuma haɗin gwiwar Nijeriya da Turkiyya zai taimaka wajen musayar ilimi da zai tabbatar da cewa masu sana’ar hannu sun samu ƙwarewar da ake buƙata

Kazalika, Dokta Ogun ya yi tsokaci kan batun cibiyoyin koyar da sana’o’in hannu a Nijeriya daga kasashen waje wanɗanda ba su da lasisi, inda ya ce ITF na ƙoƙarin kawo karshensu la'akari da asarar kuɗaɗen shiga da suke jawo wa hukumomin ba da horarwa na cikin gida.

Za mu kafa sabbin ka'idoji a fannin horar da masu sana'ar hannu a Nijeriya, tare da takwarorinmu na Turkiyya sannan za mu tabbatar da cewa duk wani shirin ITF ya kai ga samun sahihin takaddar shaida da za a yi amfani da ita a ko'ina a duniya, in ji shi.

TRT Afrika