Kungiyar masu baje-kolin fina-finai ta Nijeriya CEAN ta bayyana cewa ta samar wa kasar kudaden shiga da suka kai Naira miliyan 482 daga dukkan gidajen sinima a kasar a watan Yuli.
Shugaban CEAN na kasa Mista Opeyemi Ajayi ne ya bayyana hakan a yayin wata hira da kamfanin dillancin labarai na Nijeriya (NAN) ya yi da shi a jihar Legas da ke kudu maso yammacin kasar.
Ajayi ya bayyana cewa jimillar masu kallo da suka shiga gidajen sinima a watan Yuli a fadin kasar baki daya ta kai dubu mutum 218,395.
Shugaban ya shaida wa NAN cewa yanayin yawan mtane da suka kai ziyara gidajen Sinima a cikin watan Yuli ya biyo bayan tsawon lokacin hutu da aka samu a cikin watan.
“Mun samu jimillar ciniki na Na Naira Miliyan 482,528,117 a watan Yuli daga masu kallo 218,395 a gidajen sinima," a cewar Mista Ajayi.
Shugaba ya bayyana cewa idan ana samun mutane da dama wadanda ke amfani da lokutan shakatawarsu wajen kai ziyara gidajen kallo na sinima, ba shakka bangaren zai taka muhimmiyar rawa wajen samar wa kasar kudaden shiga.
"Babu shakka gidajen Sinima a Nijeriya sun tabarbare amma muna kara karfafa gwiwar 'yan kasar da su rungumi dabi'ar ziyartar sinima," in ji shi.