Nijeriya ta janye karar da ta shigar tana neman kamfanin Eni SpA ya biya ta dala biliyan 1.1, wanda hakan ya kawo karshen ja in jar da ake yi a kotun Italiya game da batun cin hanci da rashawa kan rijiyar mai ta Eni.
Kasar ta Yammacin Afirka za ta janye karar daga gaban kotun Italiya ba tare da wani sharadi ba kuma nan da nan, wanda hakan ba zai wuce ranar 17 ga Nuwamba ba, kamar yadda wata wasika da Bloomberg ta gani.
Sannan kasar za kuma ta hana kanta duk wata dama ta shigar da kamfanin Eni da rassansa ko manyan ma'aikatansa ƙara a Italiya game da rijiyar mai ta Eni mai lasisi OPL 245.
Kamfanin Eni ya tabbatar da samun wasika game da wannan mataki, kamar yadda ya sanar a cikin wata sanarwa inda kamfanin ya ce ya shirya aiki da gwamnatin Nijeriya don ganin an fara diban mai a rijiyar.
Ma'aikatar Shari'a ta Nijeriya ba ta samu damar cewa wani abu ba game da wannan batu.
An dakatar da ayyuka a rijiyar man ta Nijeriya sama da shekaru goma, saboda shari'a da ake ta yi.
Ana kallon wajen a matsayin wanda ya fi kowanne yawan albarkatun mai, wanda yake dauke da gangar mai miliyan 560, a wani hasashe na Eni.
Ko Eni da abokin huldarsa na Shell za su fara hakar mai a rijiyar OPL 245, hakan ya dogara kan yadda aka warware sauran batutuwa, da suka hada da neman shiga tsakani da kamfanin Eni ya kai gaban Cibiyar Sulhu ta Kasa da Kasa ta Bankin Duniya.
A shekarar da ta gabata kotu a Milan ta wanke Eni, Shell da wasu tsaffin manajoji da masu ci kan zargin aikata muggan laifuka, daga cikin har da zargin suna da masaniyar za a raba cin hancin dala biliyan 1.1 da suka biya na mallakar rijiyar man ta OPL 245.
Bayan hukuncin kotun, Nijeriya ta ci gaba da karar inda ta nemi ENi da Shell su biya ta dala biliyan 3.5 wanda shi ne asalin kudin sayen rijiyar a darajarta a 2011.