Ana ci gaba da shirye-shiryen samar da mafita tare da shugabannin makamashi na duniya kan hanyoyin da za a bi wajen samar da jarin da kamfanoni masu zaman kansu ke jagoranta, a ayyukan fasahohin makamashin da ake sabuntawa da kuma kamun iskar gas a Nijeriya.
Wakilin Nijeriya kan ayyukan sauyin yanayi, Ajuri Ngelale, ne ya bayyana haka bayan halartar wani taron koli na shugabannin majalisar ministoci da shugabannin masana'antu a gefen taron Global Energy Transition Congress da aka gudanar a Milan na Italiya.
Ngelale ya ce taron ya mayar da hankali ne kan samar da hadaddun wuraren hada-hadar kudi don samar da lamuni ga kasuwanni masu tasowa wadanda ke fuskantar sauyin yanayi.
"A hankali, muna ganin sauyi mai ma'ana game da yadda ake ƙimanta haɗarin kasuwanci da ƙima a sakamakon karuwar bala'o'in yanayi."
Ya yi nuni da cewa, masana’antar inshora, musamman a kasuwannin da suka ci gaba, suna fuskantar manyan sauye-sauye kamar gagarumin sauyi a hanyoyin da ake tantance haɗarin kasuwanci da kimar kasuwanci a yayin da ake kara samun yawaitar bala’o’in yanayi.
Wakilin Shugaban Kasa na Musamman kan Ayyukan Yanayi, Ngelale ya jaddada cewa nan gaba za a dinga tantance kamfanoni bisa la’akari da tasirin sauyin yanayi.