Nijeriya na yawan karbar bashi don  cike gibin kasafin kudi. Hoto: AA

Majalisar Zartarwar Nijeriya ta amince da karbo lamunin gata na dala biliyan daya daga Bankin Raya Kasashen Afirka AfDB, a cewar Ministan Kuɗi Olawale Edun a ranar Litinin.

Edun ya shaida wa manema labarai bayan wani taron majalisar ministocin da aka gudanar a Abuja babban birnin kasar cewa, akwai kudin ruwa kashi 2.4 kan bashin wanda aka bayar na tsawon shekara 25, amma za a daga kafa na shekara takwas idan lamunin ya wuce ba a biya ba.

“(Majalisar zartarwa ta tarayya) ta amince da wani rancen rangwame na dala biliyan daya don tallafa wa kasafin kudin kasar gaba daya da kuma amfani da shi wajen inganta samar da kudaden waje a kasar," in ji Edun, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito.

Reuters