Kongo ta jaddada kasancewarta mamba a kungiyar Organization of Petroleum Exporting Countries (OPEC) ta kasashe masu arzikin man fetur, kwanaki kadan bayan makwabciyarta Angola ta yanke shawarar fita daga kungiyar.
"Jamhuriyar Kongo tana jaddada goyon bayanta game da tsare-tsare da manufofin Sakatare Janar na OPEC da kuma OPEC+," a cewar wata sanarwa da ministan makamashin kasar Bruno Jean-Richard Itoua ya wallafa a shafinsa na LinkedIn ranar Asabar.
"Kongo za ta ci gaba da hada kai na kut da kut da dukkan mambobin kungiyar."
Nijeriya ta jaddada kasancewa mamba
Hakan na faruwa ne bayan Nijeriya ta jaddada zamanta a kungiyar OPEC inda karamin ministan man fetur Heineken Lokpobiri ya ce kasarsa ba za ta gaza wajen ci-gaban kungiyar ba.
"Hadin kanmu da kungiyar shi ne yake samar da zaman lafiya da dorewar cinikayya a kasuwar man fetur," in ji Lokpobiri a wata sanarwa da ya fitar ranar Juma'a.
"Muna tsaye tsayin-daka wajen ganin OPEC ta cim ma muradunta inda za mu ci gaba da hada gwiwa wajen kawar da duk wani kalubale da ya shafi kasarmu da ma nahiyarmu baki daya."
Ba a yi wa Angola 'adalci' ba
An bai wa Kongo, wadda ta zama cikakkiyar mamba ta OPEC a 2018, damar fitar da ganga 277,000 ta danyen fetur a kullum zuwa 2024, a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters.
Nijeriya, wadda ita ce kasa mafi girma da ke hako danyen fetur a Afirka, da Angola suna cikin kasashe da dama da aka bai wa damar fitar da danyen fetur kasa da wadda aka bai wa Kongo zuwa 2024 saboda sun gaza cika alkawuran da suka dauka a baya.
Ranar Alhamis Ministan Fetur na Angola Diamantino Azevedo ya ce OPEC ba ta yi wa kasarsa adalci ba.
Hakan ne ya sa kasarsa ta bi sahun kasashe irin su Ecuador da Qatar wurin fita daga kungiyar a shekaru goma da suka gabata.