Hukumar Kula da Lantarki ta Nijeriya ta ci tarar Kamfanin Rarraba Lantarki na Abuja Naira biliyan 1.69 saboda karbar kudin wuta da ya wuce ka'ida daga jama'a masu amfani da lantarki a babban birnin.
An fitar da bayanin tarar da ke kunshe a cikin wata takarda da hukumar ta fitar mai lamba 'Order NERC/2024/114," a shafin yanar gizonta a wani bangare na umarnin da aka bayar daga NERC a watan Satumban 2024.
Umar da ke dauke da kwanan watan 30 ga Agusta, kuma mataimakin Shugaban NERCm Musiliu Oseni, da Kwamishinan Shari'a da Kula da Lasisin Aiki, Dafe Akpeneye suka sanya wa hannu, ya bayyana gazawar AEDC na aiki da umarnin farko da aka ba shi na daina karbar kudin wuta ta hanyar hasashe.
Binciken da aka gudanar ya gano cewa AEDC ya karbi kudade da yawa sama da ka'ida daga wajen kwastomomi a tsakanin watannin Janairu da Satumban 2023, wanda hakan ne ya janyo cin tarar, wadda ta kai yawan kashi 10 na kudaden da aka karba.
A takardun tabbatar da bin daka da oda, an yi cikakken bayani kan kudaden da ya kamata a dinga karba na wuta, da kuma dalilin da ya sanya aka ci AEDC tarar, tare da ka'idojin karbar kudaden wuta.
"Hukumar ta amince da shirin cirar Naira biliyan 1.69 daga jimillar kudaden da AEDC suka samu a shekara, tn daga watan Satumban 2024, a matsayin hukuncin kin aiki da umarnin da aka bayar," in ji NERC.
An dauki matakin cin tarar ne bayan korafe-korafe daga kwastomomi da kuma binciken da ya bayyana AEDC na kara yawan kudin wuta sama da yadda doka ta tanada. An kuma umarci AEDC da ta inganta ayyukansu musamman da wadanda suke kan layin Band A, kuma su tabbatar da sanya idanu kan bayar da lantarki.