Tun a watan Mayu, matatar ta yi niyyar sayen gangar man fetur miliyan 24 daga Amurka na tsawon shekara guda. /Hoto: Reuters

Matatar mai ta Dangote da ke Legas za ta soma shigo da ɗanyen man fetur daga ƙasar Brazil.

Jaridar Bloomberg ta ruwaito cewa ɗanyen man da za ta soma shiga da shi ƙasar zai zama ƙari kan wanda take shiga da shi daga wasu ƙasashen waje.

Jaridar ta ruwaito cewa matatar man ta Dangote wadda har yanzu ba ta samun isashen ɗanyen man da za ta tace, za ta samu ganga miliyan ɗaya ta ɗanyen mai daga Brazil a wata mai zuwa.

Jaridar ta bayyana cewa an yi zaton kafa matatar mai ta Dangote zai kawo ƙarshen dogaro da ɗanyen man fetur da Nijeriya ke shigowa da shi daga ƙasashen waje, amma tuni matatar ta shigar da miliyoyin gangar ɗanyen mai cikin ƙasar.

Haka kuma jaridar ta ce a watan Yulin nan, matatar ta Dangote ta sayi gangar ɗanyen man fetur na Amurka miliyan biyar wanda ake shirin kai shi Nijeriya a watan Satumba.

Tun a watan Mayu, matatar ta yi niyyar sayen gangar man fetur miliyan 24 daga Amurka na tsawon shekara guda.

A kwanakin baya ne dai kamfanin na Dangote ya koka kan yadda ba ya samun isashen ɗanyen man fetur daga kamfanonin da ke haƙo fetur ɗin a Nijeriya.

Kamfanin ya zargi manyan kamfanonin mai da hana matatar ɗanyen man fetur ta hanyar sayar da man fiye da farashin gwamnati ko kuma iƙirarin cewa babu ɗanyen man, wanda hakan yake tilasta wa kamfanin shigo da mai daga ƙasashen waje.

TRT Afrika da abokan hulda