Manja da Nijeriya ke shiga da shi daga kasar Malaysia - daya daga cikin manyan kasashe da ke samar da man ya ƙaru da kashi 65.3 cikin 100 a cikin wata taran farkon shekarar 2023 duk da faduwar darajar Naira da kasar ke fama da shi a halin yanzu, a cewar alkaluman hukumar samar da manja ta Malaysia.
An samu karin ton 234,324 daga tsakanin watan Janairu zuwa Satumban 2023, daga ton 141,786 a bara, hakan na nuni da cewa an samu karin tan 92,538.
A watan Yuni ne Babban Bankin Nijeriya ya sabunta takardar kudin kasar don wadatar da al'umma a wani mataki na daidaita farashin dala a hukumance da kuma a kusuwar bayan fage.
Tun daga lokacin darajar kudin Naira ta ragu da kashi 62 cikin 100, matakin da ya haifar da ƙari wajen shigar da kayayyaki idan aka kwatanta da sauƙin da ake samu, a cewar masana.
''Karin kudin shiga da manja da Nijeriya ke yi daga Malaysia zai ci gaba da ƙaruwa a halin yanzu saboda jarin da muke zubawa a masana'antar har yanzu bai taka kara ya karya ba," kamar yadda babban Manajan kamfanin Palmtrade and Commodities Development Nigeria Ltd Henry Olatujoye ya shaiwa da Jaridar Business Day.
“Mun Kiyasta cewa ana amfani da tan miliyan 2.4 na manja a cikin gida a duk shekara, kuma wadanda ke kan gaba wajen samar da manja a Nijeriya – Okomu da Presco da dai sauran su, ba sa iya samar da ton din da ya kai 800,000 a kowace shekara.
"Idan muka kiyasta har da kananan manoman da suke ba da gudunmawar ton miliyan daya, har yanzu muna da gibi idan aka kwatanta da bukatar da ake da ita," in ji Olatujoye.
Ma’aikatar Aikin Gona ta Amurka (USDA) ta bayyana cewa noman kwakwar Manja a Nijeriya ya kai ton miliyan 1.4 a shekarar 2022, adadin da ya karu da kashi 9 cikin 100 idan aka kwatanta da 2020 zuwa 2021 lokacin da noman ya kai ton miliyan 1.28.