Man fetur ɗin matatar Dangote na tasiri kan kasuwannin Turai — OPEC

Man fetur ɗin matatar Dangote na tasiri kan kasuwannin Turai — OPEC

A baya dai Nijeriya ta shafe gwamman shekaru tana dogaro da shigowa da man fetur daga ƙetare.
Man fetur ɗin matatar Dangote na tasiri kan kasuwannin Turai in ji OPEC.

Ƙungiyar Ƙasashe Masu Arziƙin Mai (OPEC) ta ce man fetur ɗin da matatar Dangote ke samarwa yana tasiri kan kasuwar man fetur a ƙasashen Turai.

Matatar man Dangote wadda ta fara aiki a watan Janairun shekarar da ta gabata dai ta fara samar da man fetur ne a watan Satumban bara, bayan Nijeriya ta shafe shekaru tana dogaro kan tataccen man fetur daga ƙetare.

Matatar man ta Dangote ta fitar da man fetur da man gas da kuma na jiragen sama zuwa ƙasashe a ciki da wajen nahiyar Afirka.

Wani rahoton da ƙungiyar ta OPEC ta fitar ranar Laraba ya ce kafa matatar man Dangote ya rage yawan man fetur da ake shigarwa Nijeriya.

“Da alama yadda sabuwar matatar man Dangote ke ƙara faɗaɗa aikinta da kuma fitar da man fetur zuwa kasuwar duniya zai sake ƙara tasiri kan kasuwar man fetur a Turai,” in ji rahoton.

“Ci-gaba da samar da man fetur daga Nijeriya, ƙasar da ta daɗe tana dogara kan shigowa da tataccen man fetur daga ƙetare domin biyan buƙatar cikin gida, zai ci gaba da ƙara yawan man fetur a kasuwannin duniya, lamarin da zai janyo neman sabbin wuraren kaiwa da kuma sauya yadda za a tafiyar da ƙarin nan gaba,” in ji rahoton.

TRT Afrika da abokan hulda