Mataimakin shugabankasa, Kashim Shettima, ne ya jagorancin zaman majalisar tattalin arzikin kasar:Hoto/Twiiter/Kashim Shettima

Majalisar Tattalin Arzikin Nijeriya ta ba da shawarar janye ƙudurin yi wa dokokin haraji garambawul daga majalisar dokoki ƙasar domin bayar da damar tattaunawa da fahimtar juna tsakanin masu ruwa da tsaki kan lamarin.

A wata sanarwar da ya wallafa a shafinsa na X, mataimakin shugaban Nijeriya, Kashim Shettima, wanda ya shi ne shugaban majalisar tattalin arzikin ƙasar, ya ce majalisar ta ba da shawarar ne bayan shugaban kwamitin yi wa tsarin harajin ƙasar garambawul, Taiwo Ayodele, ya gabatar mata da ƙudurin.

Majalisar ta buƙaci kwamitin ya tattauna da masu ruwa da tsaki game da sauye-sauyen da ake son yi wa dokokin harajin ƙasar domin su cim ma matsaya a kan lamarin.

A kwanani baya ne kwamitin yi wa dokokin harajin ƙasar garambawul ya miƙa wani ƙuduri da zai bai wa jihohin da suka fi tara haraji na VAT damar samun kaso mai tsoka daga asusun raba kuɗaɗen harajin VAT na ƙasa.

Gwamnonin arewacin kasar sun nemi majalisar dokokin kasar ta yi watsi da kudurin yi wa dokokin harajin kasar garambawul:Hoto/Twiiter/Kashim Shettima

Sai dai gwamnonin jihohin arewacin ƙasar suna ganin wannan ƙudurin zai bai wa jihohin da ke da kamfanoni masu sarrafa abubuwa ƙarin kuɗi ne fiye da jihohin da ke da al’umma masu sayen ababen da ake biyan harajin VAT a kansu.

Wannan ne ya sa jihohin arewacin ƙasar suka yi kira ga majalisar dokokin ƙasar ta yi watsi da ƙudurin yi wa dokokin harajin ƙasar garambawul.

Raba wutar lantarki

Shugaban Majalisar Tattalin Arzikin Nijeriya, Kashim Shettima, ya ce majalisar za ta ɗauki matakan gaggauta rarraba wutar lantarki ta ƙasar ta yadda za a kauce wa irin matsalar katsewar lantarki irin wanda ya tsunduma jihohin arewacin ƙasar cikin rashin wuta a kwanaki kaɗan da suka gabata.

Ya ce matakan raba wutar lantarkin ƙasar sun haɗa da samar da ƙananan tashoshin wutar lantarki da sola da kuma tashoshin samar da wuta masu amfani da iska.

TRT Afrika