Tsohon shugaban Ghana kuma ɗan takarar jam'iyyar adawa, John Dramani Mahama a wurin wani gangamin yaƙin neman zaɓe a Tamale. / Hoto: Reuters

Tsohon shugaban ƙasar Ghana, John Dramani Mahama, ya bayyana aniyarsa ta ƙoƙarin sake tattaunawa kan sharuɗan samun bashin asusun lamuni na duniya IMF.

Mahama ya bayyana cewa zai bunƙasa hanyoyin mallakar ayyukan albarkatun mai, da hakar ma'adinai a nan gaba, idan har ya yi nasarar samun damar sake komawa kan mulki a watan Disamba, kamar yadda ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Mahama, wanda ya riƙe mulki daga shekarar 2012 zuwa 2016 a ƙasar, zai fafata da ɗan takarar jam'iyya mai mulki, wato mataimakin shugaban ƙasa Mahamudu Bawumia.

Ɗan takarar yana da damar samun nasara idan aka yi la'akari da tsananin matsin tattalin arziƙi a Ghana, wanda ya rage farin jinin gwamnatin da ke riƙe da mulki.

"Na taɓa shiga wani shirin IMF a baya, a lokacin da nake shugaban ƙasa, kuma ina sane da cewa IMF ba ta ƙin zama a tattauna da yarjejeniya kan batutuwa,'' in ji Mahama, mai shekaru 65 a hirar da Reuters ta yi da shi.

Har yanzu dai Ghana ta gaza biyan bashin da ake bin ta a shekarar 2022, wanda ya kai dala biliyan 30 a shekarar 2022, bayan ɓullar cutar COVID-19, da kuma tasirin yaƙin Ukraine da ƙaruwar kuɗaɗen ruwa a duniya da aka samu.

Bashin IMF

Sashen mai da zinari da cocoe, ya samu tallafin dala biliyan uku na IMF a watan Mayun 2023. Sannan a watan Yunin bana ya cim ma yarjejeniya daban-daban da masu ba da lamuni, da 'yan kasuwa don sake fasalin basussukan da ake bin ƙasar tare da neman a dakatar da biyan kuɗaɗen har zuwa shekarar 2025.

Tuni dai IMF ya raba dala biliyan 1.56 da kuma dala miliyan 360 kafin zuwan watan Disamba.

Sai dai Mahama ya ce zai sake neman ƙarin kuɗaɗe daga IMF don taimakawa Ghana, don ta ci gaba da biyan basussukan da ke kanta.

Kazalika ya ce zai gyara dokar kula da harkokin kuɗi ta gwamnati don tilasta biyan bashin da ya kai kashi 60 zuwa 70 cikin 100, na ma'aunin tattalin arzikin ƙasar a GDP domin hana ƙasar ƙarbar rance mai yawa.

Haka kuma Mahama ya ce zai mutunta ƙwangilar samar da man fetur da kamfanonin haƙar ma'adinai, kuma ba zai ƙara haraji ba.

Reuters