Ministan Tattalin Arziki da Kasuwanci na ƙasar Libya Mohammed al Huwayj, ya bayyana Turkiyya a matsayin abokiyar kasuwancin Libya ''ta ɗaya'' a fannonin da suka haɗa da na ababen more rayuwa da na masana'antar mai da makamashi da kuma ci-gaban tattalin arziki.
Al Huwayj ya ce Libya na da burin haɓaka hanyoyin tattakin arzikinta cikin sauri, yana mai jaddada cewa makamashi wani muhimmin ɓangare ne da harkokin sufuri da noma da sauran ayyuka da masana'antu ke dogaro a kai.
A yayin da yake bayyana nasarar tsarin tattalin arzikin Turkiyya, ministan ya ce ''ƙwarewar Turkiyya na ɗaya daga cikin mafi kyawun misalai a cikin ɗan ƙanƙanin lokaci, kuma muna fatan cin moriyar wannan ƙwarewa.''
Kazalika Al Huwayj ya ce Libya da Turkiyya na koƙarin ƙulla yarjejeniyar cinikayya cikin 'yanci.
"Muna shirye-shiryen sabunta dukkan yarjejeniyoyin da muka ƙulla a baya da kuma yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin ƙasashen biyu tare da aƙrfafa hanyoyin zuba-jari," in ji shi.
Abokan hulɗa na tsawon lokaci
Ministan ya ƙara da cewa ƙasashen Turkiyya da Libya mambobi ne na dindindin a kwamitin tattalin arziki da kasuwanci na ƙungiyar haɗin-kan Ƙasashen Musulmi (OIC), kana suna dab da kammala yarjejeniyar hana biya haraji sau biyu.
"Za mu gana da Ministan Kasuwanci na Turkiyya da sauran ma'aikatun da abin ya shafa don kammala yarjejeniyar kasuwanci cikin 'yanci tare da warware ƙalubalen da ke tsakanin ƙasashen biyu," in ji shi.
Kazalika Ministan ya ce 'yan kasuwar Libya da kuma yawancin kamfanoni masu zaman kansu a ƙasar suna ba da fifko ga Turkiyya, kuma tun da kamfanonin suna ɗaya daga cikin sashen ci gaba na tattalin arzikin Libya, mu kuma a ɓangarenmu za mu fi mayar da hankali kan Turkiyya a matsayin ɗaya daga cikin abokan hulɗarmu na tsawon lokaci.''
Ya ce Libya na fatan ganin Turkiyya ta shiga aikin haƙo fetur da tacewa da kuma sarrafa shi.
"Muna maraba da dukkan kamfanonin Turkiyya, sannan ma'aikatarmu za ta samar da dukkan abubuwan da suka dace,'' in ji shi.