Libya ta musanta zargin tattauna batun ɗanyen mai da kamfanin Ɗangote / Hoto:/Twitter/Dangote

Kamfanin mai na ƙasar Libya (NOC) ya musanta zargin ƙulla wata yarjejeniya ta samar da ɗanyen mai ga matatar mai ta Dangote a Nijeriya.

NOC ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi a shafinsa na X, yana mai mayar da martani bisa ga iƙirarin da wani babban jami’i a kamfanin Dangote ya yi cewa ƙasar Libya na ci gaba da tattaunawa kan yarjejeniyar samar da ganga 650,000 ta ɗanyen mai a kowace rana ga matatarsu.

''Kamfanin mai na ƙasa ya musanta batun ƙulla wata tattaunawa kan samar da ɗanyen mai da wata matatar mai a Nijeriya,” in ji sanarwar NOC.

Kazalika kamfanin ya ce, ya himmatu wajen mutunta yarjejeniya da takwarorinsa na ƙasashen duniya sannan yana ''bin dokoki da tsarin sayar da ɗanyen mai na ƙasar Libya kana ba ya ya yarda ya karkatar da alƙiblarsa zuwa wani wuri.''

Libya tana fitar da ɗanyen mai da ya kai ganga miliyan 1.28 a kowace rana, a cewar NOC.

Wannan bayani ya haifar da ruɗani a kasuwannin man fetur na duniya, la'akari da hasashen manazarta kan cewa yarjejeniyar ka iya yin tasiri wajen ƙara farashin mai da kuma samunsa a kasuwanni.

Reuters