Hukumar hana fasa-ƙwauri ta Nijeriya (Kwastam) ta ce ta kama kwantena 20 dauke da durom 1,600 na daskararren gurɓataccen tumatir da aka yi fasa-ƙwaurinsa zuwa ƙasar daga Sifaniya.
Da yake gabatar wa 'yan jarida gurɓataccen tumatirin a ranar Juma'a, Bashir Adewale Adeniyi, shugaban riƙo na hukumar kwastam, ya ce a ranar 8 ga watan Agustan 2023 ne jami'an hukumar suka kame kayan a tashar jiragen ruwa ta PTML da ke Apapa a birnin Legas.
Ya kuma ce an kama mutum ɗaya mai suna Okonkwo Oliver Izunna da ake zargi da hannu a yunƙurin fasa-ƙwaurin gurɓataccen tumatirin.
Ya ce an ƙiyasta kuɗin gurɓataccen tumatirin a kan Naira miliyan goma sha shida da dubu ɗari biyu da sha ɗaya da ɗari bakwai da ashirin da biyar, (N116,211,725.73), ya ce wadanda suka shigo da tumatirin sun yi ɓad-da-bamin sunansa.
Bashir Adewale ya ce gurbataccen tumatirin abu ne da ke da matuƙar haɗari ga lafiyar al'umma, kuma hukumar ta miƙa shi tare da wanda ake zargin yin fasa-ƙwaurinsa ga Hukumar da ke Kula da Ingancin Kayan Abinci da Magunguna ta Nijeriya, wato NAFDAC.
A lokacin da yake karbar kwantenonin gurɓataccen tumatirin, Daraktan da ke kula da fannin bincike da tabbatar da bin doka da ƙa'ida na NAFDAC, Francis Ononewu ya ce gurɓataccen tumatirin da aka kama yana da matuƙar yawa domin a daskare yake cikin durom-durom har 1,600.
Ya ce inda kayan sun kai ga cikin al'umma za su yi illa matuƙa domin a duk durom guda za a iya fitar da dubban ƙananan gwangwani na tumatir.
Ya ce masu fasa-ƙwaurin sukan zuba tumatirin ne a ƙananan gwangwani sai su sanya masu kwanan wata da zai nuna kamar yanzu aka yi su, ba su gurbata ba.
"A haka sai a kai su kasuwa a sayar wa jama'a gurbataccen tumatirin mai illa, ba tare da saninsu ba, don haka muna yabawa hukumar Kwastam da wannan gagarumin kame da suka yi," in ji shi.