Kamfanin Olam na kasar Singapore (OLAG.SI), a ranar Litinin ya musanta rahotannin da aka watsa a kafafen yada labarai na Nijeriya a makon jiya, kan zargin cewa reshen kamfanin da ke kasar na da hannu a badakalar biliyoyin daloli.
Jaridar Daily Nigerian da Prime Business Africa sun ruwaito cewa jami’an tsaro na sirri a Nijeriya na binciken rukunin kamfanonin Olam a kasar da sauran sassan kamfanin da ke kasashen ketare da kuma wasu kamfanoni masu alaka da su kan badakalar sama da dala biliyan 50.
"Kamfanin ya musanta zarge-zargen rahotannin," a cewar wata sanarwa da ya fitar, kazalika Olman ya ba da umarni ga kwamitin bincikensa da ya sake yin nazari kan lamarin.
Hannun-jarin kamfanin ya fadi da kashi 7.8 cikin 100 kan farashin dala 1.180 da misalin karfe 06: 27 agogon GMT a ranar Litinin, bayan kasa da ya yi a watanni hudu na farkon shekarar nan kan dala 1.150.
Kazalika rahotannin sun yi zargin cewa akwai wasu 'yan Nijeriya da ke gudanar da ayyukansu a matsayin 'daraktoci na boge a kamfanonin'', sannan hukumomi sun gano wasu cibiyoyin hada-hadar kudade da ke da alaka da Olam.
An wallafa labarin rahoton ne a ranakun 7 da 9 na watan Satumba shekarar 2023.
Kamfanin Olam ya ce reshensa da ke Nijeria ya amsa bukatun karin bayani daga hukumomin Nijeriya kuma za su ci gaba da ba da hadin kai.