Jirgin ruwan Turkiyya mai bincike, Oruc Reis ya isa gaɓar tekun Somalia don gudanar da bincike kan albarkatun mai da iskar gas, in ji Ministan Makamashi da Albarkatun Ƙasa na Turkiyya, Alparslan Bayraktar.
"Oruc Reis ya isa wajen da zai yi aiki bayan tafiyar keta nahiyoyi," in ji Bayraktar a saƙon da ya wallafa a shafin X ranar Juma'a.
Ministan tare da Shugaban Ƙasar Somalia Hassan Sheikh Mahamud za su halarci bikin tarbar jirgin.
A farkon watan nan ne jirgin ya tafi Somalia don gudanar da binciken mai da albarkatun iskar gas a yankuna uku da Turkiyya ta samu lasisin neman mai.
Oruc Reis zai yi aikin binciken mai da iskar gas da fasahar 3-D a gaɓar tekun Somalia.
Ana sa ran aikin zai shafe watanni bakwai yana aiki da zai ƙunshi tattara bayanai game da mai da iskar gas.
Za a yi nazari kan bayanan da aka samu a Ankara don bayyana a waɗanne wurare ne za a iya hako man.
Yarjeniyoyin fahimtar juna
A farkon wannan shekarar, Turkiyya da Somalia sun sanya hannu kan yarjeniyoyin fahimtar juna a tsakanin ma'aikatu da gwamnatocinsu.
A ƙarƙashin waɗannan yarjeniyoyi, Kamfanin Mai na Turkiyya, ya samu lasisin binciken albarkatun mai a wurare uku da ke tekun Somalia.
Ma'aikatar na shirin gudanar da bincike a dukkan wuraren uku, wanda kowane na girman murabba'i 5,000.