Jamhuriyar Benin ta janye takunkumin hana fitar da mai daga Nijar na wucin gadi/ Hoto: TRTAfirka

Jamhuriyar Benin ta janye matakin da ta ɗauka na hana fitar da ɗanyen man fetur daga Nijar zuwa ta tashar jiragen ruwanta.

Ƙasar, wacce ke yankin yammacin Afirka ta amince a gudanar da zaman tattaunawa tsakanin kasashen biyu, kamar yadda ministan ma'adinai na Benin ɗin ya bayyana a ranar Laraba.

A makon da ya gabata ne ƙasar Benin ta sanar da dakatar da lodin man fetur ɗin Jamhuriyar Nijar wanda za a dinga fitar wa zuwa ƙasashen ƙetare daga iyakar Sème-Kraké, biyo bayan takun saƙar da ya ɓarke tsakaninta da makwabciyarta ta.

Ƙasar ta buƙaci gwamnatin mulkin sojin Nijar ta sake buɗe kan iyakokinta ga kayayyaki tare da daidaita hulɗar da ke tsakani kafin a maido da jigilar ɗanyen man gadan-gadan.

''Mun yanke shawarar ba da izinin yin lodin jirgin mai na farko a cikin ruwanmu. Ko da yake, yana da muhimmaci a sani cewa wannan izinin na wucin gadi ne,'' a cewar Ministan makamashi, da ruwa da ma'adinai na Benin Samou Seidou Adambi ga manema labarai bayan ganarwasa da abokan hulɗa na kasar China.

'' Benin ta ƙudiri aniyar mutunta dukkan yarjejeniyoyin da aka ƙulla na aikin bututun,'' a cewar Adambi yana mai kari da cewa, ƙasar ta shirya gudanar da wani taro domin duba ''batutuwan gaggawa'' da suka shafi yadda ake gudanar da ayyukan bututun na fitar da mai.

Dangantaka tsakanin Benin da Nijar ta yi tsami ne tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ƙasar a cikin watan Yulin 2023, lamarin da ya sanya Ƙungiyar Raya Tattalin Arzikin Ƙasashen Yammacin Afrika (ECOWAS) ta ƙaƙaba wa Nijea takunkumi sama da watanni shida.

An yi hasashen cewa al'amura musamman na harkokin kasuwanci za su daidaita a yankin bayan ɗage takunkumin da ECOWAS ta yi a watan Fabrairu.

Sai dai Jamhuriyar Nijar ta ƙi buɗe iyakokinta da maƙociyarta don ci gaba da safarar kayayyaki daga Benin, ba tare da ta fada wa Benin a hukumance dalilin yin hakan ba, in ji shugaba Patrice Talon a wata sanarwa da ya fitar a makon jiya.

A farkon makon nan ne ita ma Nijar ɗin ta mayar da martani, inda Firaiministan ƙasar Mahamane Lamine Zeine ya ce ƙasarsa za ta ci gaba da rufe iyakarta da Benin saboda a cewarsa Benin ɗin ta saɓa yarjejeniyar haɗin gwiwar da suka ƙulla kan batutun man fetur.

Ya kara da cewa Nijar ba za ta buɗe iyakarta da Benin gaba ɗaya ba saboda dalilan tsaro.

Wani kamfanin China ne ya yi aikin shimfiɗa bututun man fetur ɗin Nijar mai nisan kilo mita 2,000 daga rijiyoyin mai na Agadem zuwa iyakarta da ƙasar Benin wanda aka buɗe a watan Nuwamba a hukumance, wanda ya haɗa rijiyoyin man Agadem na Nijar da tashar ruwan Cotonou na Benin.

Ita dai Benin tana da teku kuma hakan zai sa a loda man a manyan jiragen ruwa cikin sauƙi.

Nijar dai tana zargin cewa Benin tana haɗa baki da dakarun Faransa kuma ma har ta ba su masauki a cikin ƙasarta waɗanda za a yi amfani da su wajen cutar da Nijar ɗin. Sai dai ƙasar Benin ta musanta wannan zargi.

Reuters