Nijeriya ta halarci Taron Kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmi a Saudiyya / Hoto: Aso Villa

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya gana da mataimakin shugaban Bankin Raya Kasashen Musulmai (IsDB) Mansur Mukhtar a ranar Litinin din nan a birnin Makka na Saudiyya, in ji sanarwar da kakakin Tinubu Ajuri Ngelale ya fitar.

Sai dai babu wasu cikakkeun bayanai kan nawa Nijeriya ta bukata daga bankin ba.

Sanarwar ta rawaito Tinubu na cewa "Muna da gibin gaske a bangaren tasoshin jiragen ruwa da cibiyoyin samar da makamashi da ayyukan noma."

Ya ce "Wannan gibi na bayar da damar da babu irin ta ga masu zuba jari a wannan bangare, sama da ko ina a nahiyar."

A ranar Juma'a, Nijeriya ta kulla yarjeniyoyin zuba jari da dama da Sadiyya, da suka hada da alkawarin da gwamnatin Saudiyya ta yi na saka wasu makudan kudaden kasar waje don taimakawa kudin Nijeriya.

A karkashin Tinubu, Nijeriya ta fara daukar matakin gaske na tsawon shekaru, inda ta kawo karshen tallafin man fetur da takaita kasuwancin kudaden kasashen waje, a wani bangare na matakan bunkasa tattalin arziki.

Mataimakin shugaban IsDB Mukhtar ya ce a shirye bankin yake ya yi aiki da gwamnatin Nijeriya tare da taimakawa wajen gudanar da manyan ayyuka a ƙasar, wanda ka iya samun kaso mai tsoka daga dala biliyan 50 da bankin ya ware don zuba jari a Afirka.

TRT Afrika