Tun daga farkon shekarar 2024  Ghana take ta samun saukin tsadar kayayyaki a kasar./ Hoto: Ghana News Agency

Hauhawar farashin kayayyaki a Ghana a watan Yunin 2024 ta ragu zuwa kashi 22.8 cikin 100, adadi da ke zama mafi ƙaranci da aka taɓa samu a ƙasar tun watan Afrilun 2022.

A watan Mayu, hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar ta ragu zuwa kashi 23.1 cikin 100 kana tun daga farkon shekarar 2024 ake ta samun sauƙin tsadar kayayyaki a ƙasar.

Alƙaluman wata zuwa wata kan hauhawar farashin kayayyaki a Ghana sun yi nuni da cewa, a watan Yunin 2024, ƙasar ta samu ragin kashi 2.9 cikin 100 na tsadar kayayyaki daga kashi 3.2 da aka samu a watan Mayu.

Bisa ga bayanan da Hukumar Ƙididdiga ta Ghana ta fitar, hauhawar farashin abinci a ƙasar ta ƙaru da kashi 24 daga kashi 22.6 cikin 100 da aka samu a watan Mayun 2024.

An samu ƙarin maki 0.3 ne kawai daga kashi 22.5 a hauhawar farashin kayayyaki a hasashen watan Yunin 2024 da masana tattalin arzikin a kasuwar hada-hadar kuɗaɗe suka yi.

Sassauta manufofin kuɗi a Ghana

Yayin da aka soma samun ragi a hauhawar farashin kayayyaki a watanni huɗun ƙarshe na 2023, Bankin Ghana (BoG) ya yanke shawarar sassauta manufofi da tsare-tsarensa kan kuɗi, inda a watan Janairun 2024 ya rage tsarin daga kashi 30 zuwa 29 cikin 100.

Bayan wannan yunƙuri ne, a watan Fabrairun 2024 aka ɗan samu ragin hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar zuwa kashi 23.2.

Ko da yake a watan Maris, hauhawar farashin kayayyaki a ƙasar ta ƙaru zuwa kashi 25.8 cikin 100 yanayin da ya sanya Bankin Ghana dakatar da matakin sassauta manufofinsa na kuɗi da ya ɗauka.

Duk da wannan ragi da aka samu tun daga watan Maris a ƙasar, ana hasashen cewa za a ƙara samun ƙarin ragi idan kwamitin manufofin kuɗi na BoG ya sake zama a ranar 29 ga watan Yulin.

A yanzu haka dai Ghana tana ɗaya daga cikin mafi girman kasuwa da ke samun riba a Afirka la'akari da ɗarajar farashin kayayyaki na kashi 29 cikin 100 da ta samu.

TRT Afrika