Gwamnatin Nijeriya ta cire harajin VAT da kudin fito na gas din girki

Gwamnatin Nijeriya ta cire harajin VAT da kudin fito na gas din girki

Ana sa ran wannan mataki zai sauko da farashin gas din a fadin kasar.
A farkon watan nan na DIsamba ana sayar da kilo 12.5 na gas din girki a NIjeriya kan kudi Naira 11,800. Hoto: AP / Photo: AFP

A wani mataki na kokarin rage farashin gas din girki a Nijeriya (LPG), gwamnatin tarayyar kasar ta janye harajin VAT da kudin fito daga gas din girki da ake shigo da shi kasar daga kasashen ketare.

Ana sa ran wannan mataki zai sauko da farashin iskar gas din a fadin kasar.

Ma'aikatar Kudi ta Nijeriya ce ta sanar da wannan mataki a cikin wata wasika mai kwanan watan 28 ga Nuwmaban 2023, wadda aka aika ga hukumomin da matakin ya shafa da suka hada da ofisoshin Mai Bayar da Shawara ga Shugaban Kasa Kan Makamashi da Kwanturola Janar na Hukumar Kwastan da Shugaban Hukumar Tattara Haraji ta Tarayya.

Wasikar da Ministan Kudin Nijeriya kuma Mai Kula da Tattalin Arziki Wale Edun ya sanya wa hannu, ta bayyana kudirin Shugaba Tinubu na inganta yanayin zuba jari a kasar,

Wasikar ta ce "Duba ga kokarin Shugaba Bola Tinubu na inganta yanayin zuba jari a Nijeriya da kara yawan shigo da gas din LPG don biyan bukatar jama'a da sauko da farashi da inganta yanayin yin girki, Ina mai aiwatar da umarnin da shugaban kasa ya bayar a ranar 28 ga Yuli, 2022."

Wasikar ta kuma yi karin haske kan cewar LPG na amfani da lambobin 'HS Codes' da aka janyewa harajin VAT da kudin fito.

Bayan daukar wannan mataki, an umarci hukumar kwastan ta Nijeriya da ta janye duk umarnin biyan kudade da ta aike wa 'yan kasuwar da ke shigo da albarkatun LPG tun daga watan Agustan 2019.

Baya ka iskar gas din ta LPG, an kuma cire harajin na VAT da kudin fito ga tukunyar gas, nau'urar gane zirarar ga da, bututun karfe, bawul da janarata mai aiki da gas da tankunan dakon iskar gas din.

A farkon watan nan na DIsamba ana sayar da kilo 12.5 na gas din girki a Nijeriya kan kudi Naira 11,800.

Kamfanin samar da iskar gas na Nijeriya (NLNG) ne ke samar da kaso 40 na LPG da ake bukata a kasar inda ake shigo da sauran kaso 60 daga kasashen waje.

TRT Afrika da abokan hulda