Kasuwar Mile 12 babbar kasuwa ce da ake sayar da kayan gwari, wato kayan miya da ake kai wa yawanci daga arewacin kasar. Hoto: TRT Afrika

Gwamnatin Jihar Legas da ke kudu maso yammacin Nijeriya ta rufe Kasuwar Kayan Gwari ta Mile 12 a ranar Juma’ar nan, kan dalilai na rashin tsafta da gurɓata muhalli, kamar yadda hukumomi suka ce.

“Mun wayi gari da misalin ƙarfe huɗu na asubahin yau Juma'a jami'an hukumar duba gari ta jihar Legas suka isa kasuwar kayan abincin inda suka sanya mukullai suka garƙame ta,” kamar yadda wasu ƴan kasuwar suka shaida wa TRT Afrika.

Kasuwar Mile 12 babbar kasuwa ce da ake sayar da kayan gwari, wato kayan miya da ake kai wa yawanci daga arewacin kasar da ma ƙasashe maƙwabta irin su Ghana da Jamhuriyar Benin da Togo da sauran su.

Kasuwar ta shahara sosai, sannan tana daga cikin manyan kasuwannin Jihar Legas.

Rufe kasuwar Mile 12 na zuwa ne bayan da gwamnati ta ɗauki matakin rufe wasu kasuwanni a jihar a makon da ya wuce, ciki har da katafariyar kasuwar sayar da kayan gyaran motoci ta Ladipo da ke Oshodi a Legas ɗin.

A sanarwar da ta fitar, Ma’aikatar Kula da Muhalli da Albarkatun Ruwa ta Jihar Legas ta ce ta bai wa hukumar kula da tsaftar muhalli umarnin rufe kasuwar saboda yadda ake zubar da shara da datti barkatai da ƙona sharar da barin datti na toshe magudanan ruwa da kuma ajiye motoci ba bisa ƙa’ida ba da ke jawo cunkoso da tare tituna.

Kwamishinan Muhallin Kunle Adeshina ya ƙara da cewa “Rufe Kasuwannin Mile 12 da Owode Onirin zai bai wa masu ruwa da tsaki damar bibiyar yanayin da inganta lafiyar al’umma da tsaftace muhalli a yankunan kasuwannin.

“Yanayin da kasuwannin ke ciki ya munana ta yadda dole a dauki matakin yin wani abu a kan lamarin.

"Za mu tafka asara"

Sai dai wasu ƴan kasuwar Mile 12 sun yi ƙorafin cewa rufewar za ta jawo musu ɗumbin asara ta kayan miyan da ke jibge a kasuwar.

'Yan kasuwar sun ce rufewar za ta jawo musu asarar kayan gwarin da suke sayarwa. Hoto: TRT Afrika

Daya daga cikin shugabannin kasuwar Alhaji Dauda Tarai, ya shaida wa TRT Afrika cewa shugabannin kasuwar na yin duk abin da ya dace wajen tsaftace ta.

Ya ƙara da cewa “kasuwar kayan gwari ba daidai take da ta kayan ƙarafa ko kayan sawa ba, domin kayan gwari kaya ne da ba sa jure ajiya, kuma rufe kasuwar zai janyo mana asarar ɗimbin dukiya.

Ya ce yanzu haka shugabannin kasuwar na ƙoƙarin ganawa da mahukunta a jihar ta Legas domin ganin yadda za a sake buɗe kasuwar.

TRT Afrika