A ranar Alhamis ne ma'aikatar shari'a ta Amurka ta sanar da shigar da jerin ƙararraki kan kamfanin Apple, inda take zargin sa ta kankane harkar babbar waya ta haramtacciyar hanya, ta yadda suke korar masu gasa da su, da rage haɓakar fasaha, da kuma janyo tsadar farashi.
Ƙarar da aka gabatar a kotun tarayya da ke New Jersey, ta zargi Apple da kankane kasawar babbr waya da kuma amfani da wayar iPhone wajen “aikata abin da ke karya doka tsawon lokaci.”
“Apple ta kankane masu amfani da wayoyinsa kan iPhone, yayin da yake korar masu gasa da shi daga kasuwa,” in ji mataimakiyar mai shigar da ƙara, Lisa Monaco.
Ta ce, "Ta hanyar daƙile cigaba a fagen fasahar kasauwancin da kamfanin ya gina, kamfanin yana "tsuke gaba ɗayar harkar.”
Apple ya ce ƙarar “ta kauce tsari bisa la'akari da bayanan gaskiya da kuma doka”, kuma ya ce zai “kare kansa daga zargin.”
'Kankanewa'
Ƙarar tana harar yadda kamfanin Apple yake kane-kane a mu'amalar fasaha da kasuwancin domin ya “tsatso kuɗi daga kwastomomi, da masu ƙirƙira, da masu masu wallafa, da ƙananan kamfanoni, da ma 'yan kasuwa."
Wannan ya haɗa da rage ƙarfin aikin agoguna zamani da ba na Apple ba, inda hakan ke taƙaita iya biyan kuɗi da agogon ta amfani da lalitar wasu kamfanonin, sannan da hana manhajarsa ta iMessage iya sadarwa da saƙonni tare da sauran manhajoji masu gasa.
Ƙarar na neman dakatar da Apple daga maƙarƙashiya kan fasaha da ke gasa da manhajojinta– a ɓangarori kamar da kwaranye, aika saƙonni, da biyan kuɗi ta dijital– da kuma hana shi cigaba da ƙulla yarjejeniya da masu ƙirƙira, da masu ƙere kaya, wanda ka ba ta damar “samu, riƙewa, da haɓaka ƙarfinta na kankane kasuwa.”
An gabatar da ƙarar ga ofishin babban mai shigar da ƙara na jihohi 16, wanda hakan wani misali ne na baya-bayan nan na yaƙi da kankanewa manyan kamfanoni a harkokin kasuwanci, irin wanda ak yi kan Google, da Amazon da sauran manyan kamfanoni.
Ƙarar ta zargi Apple da cajin kuɗin da ya kai dala $1,599 kan kowace iPhone, kuma tazarar kan kowace waya ta zarce ninkin yadda sauran kamfanoni a masana'antar way ke samu.